Shugabar da ke kan mulki Dalia Grybauskaite na da gagarumin goyon baya a kuriar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar.
Shugabar ta samu wannan tagomashi ne saboda adawar da take nunawa ga mamayar da Rasha ta yi a Crimea.
Da kuma yadda shugabar take kokarin ganin an kara yawan sojojin NATO a Lithuanian.
Sai dai kuma ba a san ko za ta samu gagarumar nasara kai tsaye ba a zagayen farko na zaben idan masu zabe ba su fito sosai ba. ABNA.