18 Nuwamba 2026 - 08:41
Source: ABNA24
Sheikh Zakzaky (H): Tabbatan Addinin Musulunci Muka Ce Muke So, Kuma Akan Haka Za Mu Tsaya Ƙyam

A ranar Lahadi, 5 ga Jimadal Akhir 1448 (15/11/2026), Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya rufe Mu’utamar na iyalan Shahidai karo na uku, a gidansa da ke Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa:Jagora (H) ya fara da jajen Shahadar Sayyida Zahra (SA), inda ya bayyana cewa, shahadar Sayyida alama ce da ke nuna cewa, shi Shahidi ba wani laifi yake aikatawa ba face ya ce Allah ne Ubangijinsa.

Da yake bayani kan mahukuntan da ke afkar da Shahada, Jagora (H) ya ce, “Mafarkin su shi ne za su kawar da mu, a nemi mu a rasa, ya zama ba ko ɗaya (daga cikinmu).” Ya jaddada cewa wannan mafarki ne da ba zai yiwu ba. Ya ce irin mummunan kisan da suka yi, musamman a waƙi’ar Buhari ta Zaria, ya nuna aniyarsu ta ganin bayan Harka har abada.

Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana yadda mahukunta ke bamu tsoro da kisa. Shi ma ya jaddada cewa; “Duk wanda ba ya son a kashe shi, kada ya shigo cikinmu. Sai wanda shi ya yarda ya ba da rai, to shi zai tsaya a tare da mu. Wanda yake son ransa, baya son ya ba da rai, to ya san inda dare ya masa. Wannan Harkar ba harkarsa ba ne. Ya je can a bashi masa da zuma.”

Yace: “Tabbatan addinin Musulunci muka ce muke so, kuma akan haka za mu tsaya ƙyam, akan haka muke ciki, har ƙarewar ajalinmu. Duk wanda ajali ya zo masa yana tsaye ƙyam, to ya yi nasara. Ba lalai ya yi Shahada ba, in mutuwa ta zo maka alhali kana tsaye ƙyam, to ka yi nasara. Ka yi musu saranda shi ne al'amari ya lalace. Su abinda suke so ka musu kenan kuma.”

A ƙarshen jawabinsa, Jagora ya yi kira ga iyalan Shahidai, da su tsaya ƙyam a kan tafarkin da iyayensu suka sadaukar da rayukansu a kansa. Ya ce, wannan shi ne abin da ya dace da su, kuma shi ne zai sa iyayensu alfahari da su. Ya kawo misalin yadda iyalan Shahidai da Shahidai masu rai suka kasance a sahun gaba wajen ci gaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙire, tare da bayyana fatansa kan yadda iyalan shahidai ke nuna jajircewa a cikin Harka Islamiyya.

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

05/Jimadal Akhir/1448

15/11/2026

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha