Lebanon: Yaƙe-Yaƙe Biyu Da Lebanon Ta Sha Sun Haifar Da Asarar Sama Da Dala Biliyan 27

Nawaf Salam: Yaƙe-Yaƙe Biyu A Lebanon Sun Haifar Da Shahidar Sama Da 9,000 Da Jikkatar 30,000
15 Satumba 2026 - 20:06
Source: ABNA24
Lebanon: Yaƙe-Yaƙe Biyu Da Lebanon Ta Sha Sun Haifar Da Asarar Sama Da Dala Biliyan 27

Yaƙe-yaƙen da Lebanon ta sha sun jawo babbar asara ta tattalin arziki da jin kai, kuma gwamnatin Nawaf Salam tana ƙoƙarin sake gina ƙasar da dawo da kwanciyar hankali ta hanyoyin diflomasiyya da taimakon ƙasa da ƙasa, tare da nanata cewa ikon gwamnati kaɗai ne ya kamata ya mallaki makamai da yanke shawarar yaƙi da zaman lafiya — ba wasu ƙungiyoyi ba. Gwamnati tana neman dawo da amincewar ƙasa da ƙasa ta hanyar yarjejeniya da IMF da ka'idojin kuɗi, da kuma dawo da haƙƙin Lebanon da ikonta ta hanyar tattaunawa da Isra'ila, ba ta hanyar yaƙi ba.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Yaƙe-yaƙen biyu da Lebanon ta sha cikin shekaru uku sun haifar da asarar sama da dala biliyan 27, tare da shahidai sama da 9,000 da waɗanda suka ji rauni 30,000 in ji Firaministan Lebanon, Nawaf Salam. Yana mai cewa: Yaƙin farko (Oktoba 2023) ya haifar da asarar kai tsaye da ta tattalin arziki kusan dala biliyan 14, yayin da yaƙin baya-bayan nan (Maris 2026) ya haifar da asarar dala biliyan 7 zuwa 9.

ji Firaministan Lebanon, Nawaf Salam ya kara da cewa: Tattalin arzikin ƙasar ya ragu da kashi 6.4 cikin 100 a wannan shekara bayan haɓakar kashi 4.2 cikin 100 a shekarar da ta gabata. Ga kuma lalacewar gidaje kusan 91,000 gaba ɗaya ko wani ɓangare a yaƙin baya-bayan nan, ban da gidaje 230,000 da yaƙin da ya gabata ya lalata. A yanzu sama da mutane 250,000 sun rasa muhallansu kuma sama da ƙauyuka da garuruwa 75 da ke ƙarƙashin mamaya sun lalace.

ji Firaministan Lebanon, Nawaf Salam: Gwamnati ba za ta iya ɗaukar nauyin sake ginawa da albarkatun da take da su ba, don haka tana dogaro kan tallafin Larabawa da kuɗi daga waje, tare da yarjejeniya da Asusun Ba da Lamuni na Ƙasa da Ƙasa (IMF) a matsayin babbar hanya don dawo da amincewar ƙasa da ƙasa.

Dangane da Kuɗi da tattalin arziki kasar ya ce: An ɗauki tsarin kashe kuɗi mai daidaito a sabon kasafin kuɗi kuma gwamnati tana bin ka'idojin kuɗi a cikin kudirin kasafin kuɗi na 2027 don hana rugujewar kuɗi. Ya roƙi majalisar da ta hanzarta tattaunawa kan dokar daidaita kuɗi da sake tsara tsarin bankuna. Domin Rrkicin ya tsananta saboda raguwar tallafin ƙasa da ƙasa; masu ba da taimako sun biya kashi 49.8 cikin 100 kawai na dala miliyan 639 da gwamnati ta nema tare da haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya, idan aka kwatanta da kashi 94.9 cikin 100 a shekarar 2024.

ji Firaministan Lebanon, Nawaf Salam ya ce: An kafa hukumar sa ido kan fannin wutar lantarki bayan shekaru 22 da rufe su, an amince da takardar manufofin wutar lantarki don buɗe hanyar zuba jari mai zaman kansa, kuma an ƙara sa'o'in wutar lantarki daga awa 7 zuwa awa 9 a rana.

Sannan ya bayyana shirye-shiryen faɗaɗa tashar jiragen ruwa da haɓaka ababen more rayuwa na tashar jiragen ruwa na Beirut don mayar da rawar tattalin arzikinta. Ya kuma bayyana wani cikakken shiri na ci gaban arewa da Akkar ciki har da farfado da filin jirgin sama na Rene Mouawad (Qlayaat), haɓaka tashar jiragen ruwa na Tripoli, aikin layin dogo da farfado da yankin tattalin arziki na musamman da baje kolin ƙasa da ƙasa na Rashid Karami.

A batun Siyasa da tsaro ji Firaministan Lebanon, Nawaf Salam: Babu kwanciyar hankali mai ɗorewa ba tare da faɗaɗa ikon gwamnati kan dukkan ƙasarta da sojojinta na asali ba kuma shawarar yaƙi da zaman lafiya da makamai ya kamata su kasance a hannun cibiyoyin doka kaɗai. Ya yi nuni da sashe na 52 na kundin tsarin mulki cewa Lebanon ba takardar tattaunawa ce a hannun wasu ba kuma gwamnati ce kaɗai ɓangaren tattaunawa da gwamnatin Sahayoniya, kuma manufofin wannan hanyar sun haɗa da kawo ƙarshen yaƙi, cikakken ficewar Isra'ila daga ƙasar Lebanon, 'yantar da dukkan fursunoni da tabbatar da komawar 'yan gudun hijira cikin aminci.

Dangane da tattaunawar Tsarin ɓangarori uku, Firaministan Lebanon, Nawaf Salam: Ya bayyana cewa wannan tsari jagora ne da manufar matakan aiwatarwa da zai kai ga ficewa Isra’ila sannu a hankali da sake kafa sojoji, ba cikakkiyar yarjejeniya ta ƙasa da ƙasa da ke buƙatar amincewar majalisar.

Gwamnatin Lebanon tana bin ƙa'idar cewa makamai su kasance a hannun gwamnati kaɗai (kamar yadda yarjejeniyar Ta'if ta tanada). Gwamnati ba ta tattaunawa da Isra'ila don wasa ba — tana tattaunawa ne domin dawo da haƙƙin Lebanon cikin hanya mafi sauƙi kuma mafi ƙarancin asara, wato ta hanyar diflomasiyya maimakon yaƙi.

Wannan ɓangaren na nuna cewa gwamnati ce ke da iko kan shawarar yaƙi da zaman lafiya, ba wasu ƙungiyoyi masu riƙe da makamai ba — musamman Hizbullah ba.

……………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha