2 Satumba 2026 - 21:45
Source: ABNA24
Financial Times: Hadin Gwiwar Makamai Masu Linzami Tsakanin Tehran Da Moscow Ya Shiga Sabon Mataki

Jaridar Ingila Financial Times a cikin wani rahoto ta yi iƙirarin cewa Rasha, a asirce, tana taimakon Iran wajen ƙera sabon nau'in makamai masu linzami na mai saurin gudu fiye da sauti; iƙirarin da idan ya kasance gaskiya, yana nuni da zurfafa hadin gwiwar dabaru da soji tsakanin Tehran da Moscow a fannin fasahohin makamai masu linzami masu ci gaba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Bisa ga rahoton jaridar Ingila Financial Times, wani shiri mai lambar sirri "C430L" ya fara tun daga shekara ta 2023 kuma yana ci gaba da gudana.

Financial Times ta yi iƙirarin cewa wasu ƙwararrun masana makamai masu linzami na Rasha a wannan aikin suna taimakon Iran wajen ƙera wani tsarin injin jet mai ƙarfi; fasahar da za ta iya ba da damar tafiyar makamai masu linzami na cikin sauri sosai.

Wannan jaridar Ingila ta yi iƙirarin cewa fasahar da ake magana akai, mai yiyuwa ne a yi amfani da ita wajen ƙera makamai masu linzami masu ci gaba na yaƙin jiragen ruwa, da kuma kai hare-hare daidai kan manufofin ƙasa.

Dangane da wannan rahoto, haɗa saurin gudu da ikon tafiya a ƙasa mai tsayi, na iya rage lokacin da tsarin tsaro zai yi don ganowa da kuma dakile irin waɗannan makamai masu linzami.

Financial Times ta kuma yi nuni da wasu takardun da ta ce bisa ga su, kamfanin fitar da makamai na gwamnatin Rasha da kamfanin NPO Mashinostroyeniya sun taka rawa wajen tsara wannan hadin gwiwa.

Wannan rahoton ya yi iƙirarin cewa injiniyoyin Rasha, kafin sanya hannu kan yarjejeniya a hukumance da ma'aikatar tsaron Iran a watan Nuwamba na shekara ta 2023, sun yi balaguro da yawa zuwa Iran, kuma a ci gaba, sun yi nazarin bayanan da suka shafi gwaje-gwajen tafiya da bayanan fasaha na shirin.

Wannan rahoto, ya kallon hadin gwiwar makamai masu linzami tsakanin Tehran da Moscow a matsayin wani ɓangare na faɗaɗa dangantakar soji tsakanin kasashen biyu, kuma ya bayyana shi a matsayin mai ban gishi in baka manda; ma'ana, a shekarun da suka gabata, Iran da Rasha sun yi amfani da damar juna a fannoni daban-daban na tsaro da soji.

Financial Times ta kuma yi nuni da wasu wasiku da ta yi iƙirarin cewa na watan Yuni na shekara ta 2026 ne, kuma ta ce tattaunawa da hadin gwiwar da suka shafi wannan shiri na ci gaba.

……………..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha