A Ranar Alhamis, 14 ga Rabi’ul Awwal, 1448, daidai da 27 ga Agusta, 2026, Harkar Musulunci a Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta shiga rana ta uku tun bayan fara gudanar da taron.
A farkon taron, an buɗe shi da addu’a wadda Sheikh Auwal Gangare ya jagoranta, sannan aka karanta Alƙur’ani tare da yin ziyarar. Malam Ishaq Garkuwa da Ammar Ɗantinka ne suka jagoranci tawagar Ittihadu-shu’ara, daga nan aka gabatar da babban baƙon da zai gabatar da jawabi.
Babban baƙon na farko ya gabatar da jawabinsa ne ƙarƙashin wata muƙala mai taken: “Muhimmancin Haɗin Kan Al’ummar Musulmi”, domin ɗaukar darasi da ƙarfafa haɗin kan Musulmi.
Sheikh Nura Khalil (Digital Imam), ya fara jawabinsa da godiya ga Allah da Ya sanya shi cikin Musulmi masu son iyalan gidan Annabi (AS), inda ya bayyana jin daɗinsa da farin cikinsa bisa maudu’in da aka ba shi. Ya ce Musulmi duk abu ɗaya ne, domin Sallah, Azumi, Zakka, Alƙibla da Hajji duk abu ɗaya ne suke yi. Ya kuma yi nuni da cewa Allah Ya bayyana a cikin Alƙur’ani cewa dukkan Musulmi abu ɗaya ne.
Yana mai cewa: “Duk mutum a duniya, tun daga ranar da ya zo duniya, yake cin albarkacin Annabi Muhammad (SAWW).” Ya ƙara da cewa dole ne mu yi imani da Allah ɗaya, kuma Annabi Muhammad (SAWW) haske ne ga duk duniya, tare da cire son rai.
Da yake magana kan halin da Najeriya take ciki, ya ce wannan sharri ne na kafirai, inda ya ba da misalin yadda tun asali kafirai suke wannan shiri. Ya ce: “Duk saboda Musulunci da muka riƙe ne, ya sa ake jefa mu cikin wannan ƙangin na wahala. Idan muka duba tarihi, za mu yarda cewa Limaman Shiriya (Iyalan Manzo) sun sha wahalhalu a hannun gwamnatocin azzalumai.” Ya ce ɗaya daga cikin manyan makircin da ake yi wa Musulmi shi ne a dubi babban malami a jawo shi cikin hauragiyar siyasar da ta ɓata.
Masu Sukar Taron Makon Haɗin Kai
Da yake magana kan masu sukar taron Makon Haɗin Kai, ya ce: “Taron Makon Haɗin Kai taro ne da ake yi domin haɗuwa, tattaunawa da magance matsalolin da suke faruwa ga dukkan Musulmi. Shi ya sa ake gayyatar kowa daga kowace mahanga.”
Ya sake jaddada wajibcin haɗuwar Musulmi a wuri ɗaya domin magance matsalolin da suke addabar al’umma, yana mai cewa addinin Musulunci bai zo da rabuwar kai ba, sai dai ya zo da haɗuwa, soyayya da girmama juna.
Kafin mai jawabi na biyu ya fara, an gabatar da kirari na musamman ga Annabi Muhammad (SAWW).
Jawabin Sheikh Shareef Ibraheem Hikima
Mai jawabi na gaba ya gabatar da jawabinsa ne ƙarƙashin wata muƙala mai taken: “Muhimmancin Haɗin Kai Musulmi.”
Babban baƙon, Sheikh Shareef Ibraheem Hikima Kano, ya fara jawabinsa da nuna jin daɗinsa bisa yadda ɓangarori daban-daban suka amsa wannan gayyata, yana mai cewa ganin yadda aka gudanar da taron ya tabbatar da cewa taron ya amsa sunansa na Haɗin Kai Musulmi.
Ya kuma gode wa Jagora Shaikh Zakzaky (H), wanda ya zama silar haɗuwarsu: Ya ce haɗuwar kan Musulmi waje guda umarnin Allah ne, da kuma soyayyar Annabi Muhammad (SAWW) da iyalan gidansa, domin ita ce hanya madaidaiciya.
Ya ce: “Saboda muhimmancin haɗin kai, mu duba yadda Manzo (SAWW) ya yi ta kira a kan a haɗa kai. Hatta kafirai ba a yaƙe su ba, sai dai suka tabbatar da ba za su haɗa kai ba, suka nemi a yi yaƙi.”
Hakazalika, ya nanata cewa: “Mu lura da wannan yaƙin da ke tsakanin Iran da Amurka. Da Musulmi suka haɗa kai, kafirci ya yi nasara a kansu? Wajibi ne mu haɗu waje ɗaya, domin umarnin Allah ne gare mu cewa dole mu haɗa kai waje ɗaya. Ya ci gaba da cewa: “Duk Baatijjane ɗan Shi’a ne, domin duk wanda ya san koyarwar Shehu Ahmad Tijjaniyya, ya san yadda ya dunga yin Tawassul da iyalan Annabi da kuma yadda ya faɗa cewa Imam Ali (AS) ne jagoransa.”
Sheikh Shareef Hikima ya yabawa Malam Zakzaky bisa jajircewarsa a tafarkin Manzon Allah (SAWW), da ƙoƙarinsa na ganin an haɗa kai waje guda, yana mai cewa: “Wannan tarbiyya ce ta bayin Allah.”
Bayan dogon bayani da ya yi, ya tabbatar da cewa duk mai son a haɗa kan al’ummar Musulmi, dole ne ya kasance mai imani da Allah da Manzonsa, tare da soyayya ga iyalan Manzo.
Malam Ishaq Misau ya yi taƙaitaccen ta’aliki, inda ya ƙara haskaka wa mahalarta jawabin Sheikh Shareef Hikima. Daga nan aka gudanar da Sallolin Magariba da Isha’i.
A ƙarshe, Sheikh Shareef Murtala Jos ya rufe taron da addu’a. Kamar yadda aka saba, an ayyana ranar Juma’a domin ci gaba da gudanar da taron.
KARIN BAYANI CIKIN HOTUNA
Daga Ali Usman Nayara
Ra'ayinka