A yau Lahadi, 17 ga Rabi’ul Awwal 1448, Jagora (H) ya gabatar da jawabin Mauludi tare da rufe taron Makon Haɗin Kai ga ɗimbin mahalarta daga sassa daban-daban na al’ummar Musulmi, a Abuja.
Jagora (H) ya gana da malamai da mahalarta taron Makon Haɗin Kan Musulmi da Harkar Musulunci ta shirya, a matsayin wani ɓangare na bukukuwan Mauludin Manzon Allah (S), a ranar Asabar, 16 ga Rabi’ul Auwal 1448 (29/8/2026), a gidansa da ke Abuja.
Makon Haɗin Kan Al’ummar Musulmi, taro ne da ake gudanarwa a birnin Abuja domin tattauna rayuwar Manzon Allah (SAWW) da ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’ummar Musulmi wanda Harkar Musulunci a ƙarƙashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta saba shiryawa a duk shekara.