Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci na Iran a wata sanarwa da suka fitar a ranar tunawa da shekaru biyu na shahadar shugaban ofishin siyasa na ƙungiyar Hamas, jagora shahidi Ismail Haniyeh, sun tabbatar da cewa daukar fansa ga jinin shahidi jagora Sayyid Ali Khamene'i da shahidi Ismail Haniyeh tabbataccen abu ne da makawa akai ko da ja da baya, kuma mayar da martani na Iran ga waɗannan laifuffuka masu girma zai kasance mai tsanani mai zartuwa.
Sanarwar ta tabbatar da cewa makircin kwace makaman ƙungiyar "Hamas" ba zai haifar da wani sakamako ba, kuma ya ci tura tun yanzu, tana yi wa duniya bishara cewa "ƙarfin Gwagwarmaya wajen fuskantar Yahudawa ba zai iya raguwa ba, kuma nasara ta ƙarshe ga Falasdinu a kan mamaya ta kusa fiye da yadda maƙiya suke zato."
Sanarwar ta yi nuni da cewa kashe jagora Haniyeh a Tehran, a lokacin da ya halarta a matsayin baƙo na hukuma a bikin rantsar da shugaban jamhuriyar Musulunci ta Iran, wani babban laifi ne da kuma take hakkin ƙa'idoji da al'adun dokokin duniya, ikon ƙasa, da amincin yankin Iran.
Sanarwar ta yi nuni da cewa bayan shekaru biyu na wannan laifi na Sahyoniyawa, kuma a cikin ci gaba da kisan kare dangi da ƙaruwar laifuffukan Sahyoniyawa a zirin Gaza, da faɗaɗa yaƙi da laifuffuka zuwa kudancin Lebanon, har zuwa fara yaƙe-yaƙe na biyu da na uku da aka kakabawa Iran, tare da harin mamugunci shugaban Amurka da sojojin ƙasarsa masu ta'addanci kan Iran, yanayin ta'addanci da laifi na wannan gwamnati ya bayyana fiye da kowane lokaci a gaban kowa.
Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun kammala sanarwarsu da nanata cewa ci gaba da goyon bayan Amurka gabaɗaya, na soji da siyasa, tare da goyon bayan wasu ƙasashen yamma da daidaitawa da haɗin kai da gwamnatocin yankin masu koma baya da tsarin mulkin Sahyoniyawa, yana sa waɗannan ɓangarori su zama abokan tarayya a cikin laifuffukan da ake aikatawa, kuma yana tabbatar da alhakinsu na duniya game da kisan kare dangi da laifuffukan yaƙi da tsarin Sahyoniyawa ke aikatawa.
Jagora Ismail Haniyeh ya yi shahada a ranar 31 ga Yuli, 2024, sakamakon wani harin Isra'ila da ya kai kan masaukinsa a babban birnin Iran, Tehran, bayan ya halarci bikin rantsar da shugaban Iran Masoud Pezeshkian.
…………….
Ra'ayinka