3 Agusta 2026 - 07:45
Source: ABNA24
Iraki: Ta Fara Babban Aiki Na Yaƙi Da Ta'addanci A Nainawa

Iraki a ci gaba da ayyukanta na kawar da sauran ‘yan ta’addan Isil tana ci gaba da sumamen aiki na mussama da bin diddigin ragowar ‘yan ta’addan a lardin Nainawa

Kamfanin Dillancin Labarai Na Ahlul-Bayt (A.S) Na Duniya – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Hukumar Yaƙi Da Ta'addanci ta Iraki ta sanar da fara wani babban aikin tsaro a lardin Nainawa don bin diddigi da tsare ragowar ƙungiyar ta'adda ta ISIL.

Ana aiwatar da wannan aiki da nufin bincika yankunan da ake zargi, gano ƙungiyoyin ISIL da suke ɓoye, da ƙarfafa tsaro da kwanciyar hankali a lardin Nainawa.

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha