3 Agusta 2026 - 19:05
Source: ABNA24
An Kammala Tattakin Yaumul Arba'in 1448h Na Zangon Malumfashi A Najeriya + Hotuna

Ƴan'uwa Musulmi Almajiran Shaikh Zakzaky (H), masu tattakin Yaumul Arba'in na zangon Malumfashi, sun kammala tattakin, wanda aka fara da safiyar yau Lahadi 18/2/1448 - 2/8/2026.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Tattakin, Wanda ya samu halartar dandazon Al'umma daga garuruwa daban-daban, kuma aka tsara shi santoci guda takwas (8).

Santar farko, daga Malumfashi zuwa Sabon Birni, Santa ta biyu, daga Sabon birni zuwa Kafur.

Santa ta ukku kuma daga Ƙafur zuwa Sabuwar Ƙasa, Santa ta huɗu, Daga Sabuwar Ƙasa zuwa Gozaki.

Santa ta biyar, Daga Gozaki zuwa Dabai, Santa ta shidda, Daga Dabai zuwa Marabar Hunƙuyi, Santa ta bakwai, Daga Marabar Hunkuyi zuwa Kwakwaran Manu, santa ta takwas, Daga Aviation Zaria zuwa cikin garin Zariya, dukkansu anfara lafiya, kuma antashi lafiya.

Dukkan santocin, wakilan ƴan'uwa na yankin ne ke gabatar da jawabin rufewa, daga kuma sai ayi addu'a a kamo hanyar dawowa gida.

MediaForumKatsina

2/8/2026

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha