3 Agusta 2026 - 18:47
Source: ABNA24
Shekh Yakub: “Mutum Ba Zai Gane Ƙimar Abin Da Yake A Hannunsa Ba Na Karantarwar Ahlul Baiti (A.S) Sai Ya Zo Karbala”...

Da yammacin yau lahadi (02/08/2026) ne Sheikh Yakub Yahya Katsina ya ziyarci Maukibin Jagoran Harkar Musulunci Sayyid Ibrahim Zakzaky (H), da ke bisa hanyar Tattaki daga Najaf zuwa Karbala, a Amudi na 1117.

Bayan Isar Sheikh Yakub a muhallin ya gaggaisa da ’yan’uwa ma'aikatan da ke khidma a Maukibin sannan daga bisani ya gabatar da taƙaitaccen jawabi. A jawabin na shi ya fara ne da godiya ga Allah bisa amsa kiran Imam Hussain (A.S) inda ya ce “Mun gode Allah da ya saka mu cikin wannan tawaga waɗanda suka karɓa kiran Imamu Hussain (A.S) domin goya wa Ahlul Baiti (A.S) baya.

A cikin ruwaya an ce (Daga Manzon Allah (S.A) yana cewa:

 "مَنْ كَثَّرَ سَوَادَ قَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ"

“idan mutane suka taru (sai) ka shiga cikinsu, ka ƙara masu duhu (idan tara ne sai suka cika goma) to kai ma za a ƙirga da kai a cikinsu”.

Sheikh Yakub ya cigaba da cewa; “Sannan kuma wannan yana tuna mana musiba da Ahlul Baiti (A.S) suka fuskanta a tsawon tarihi. Farkon Da’awa da muka fara can gida Najeriya; idan muka samu rauni, ko sarewa, ko gajiya sai mu tuna da abin da Shehu Usmanu Ɗanfodiye (R.A) ya yi. Lokacinsa babu waya, babu titi, babu alƙalami irin su biro, babu fitila, babu mota, babu koomai na wasa’il (na isar da saƙo) sai ka ga a haka mutum zai tashi daga Sokoto ya ɗauki wasiƙa ya kaita Yola ko ya kaita Maiduguri, yayi watanni kafin ya je, ya saƙa ta cikin sarƙaƙin ruƙuƙi, ya bi ta nan ya shiga ta nan, wani wurin ya haɗu da ƙorama, namun daji da sauransu. Amma a haka Allah Maɗaukakin Sarki ya hayya’a masu yanayi suka iya tsaida addini, inji shi.

To idan mutum ya kalli wannan sai ya ƙara ƙumaji, sai mu ji tunda muna da mota, muna da kaza da kaza da kaza, sai mu ƙara ƙumaji”

Har wayau ya cigaba da cewa “TO MUTUM BA ZAI GANE ƘIMAR ABIN DA YAKE A HANNUNSA BA NA KARANTARWAR AHLUL BAITI (A.S) SAI YA ZO KARBALA, sai ya zo wannan tafiyar, ya ga yadda Imamu Hussain (A.S) da jama’arsa suka yi tafiya ta tsawon mila-milai a ƙasa ba titi, ga ƙishirwa (ga shi) ba ko itaciya da ta kai tsawon da mutum da zai sha inuwa, ga mata ga yara, ga kuma babu barci babu abinci babu ma ruwan sha, (duk) dan ya raya wannan al’amari.

Alhamdulillah Allah Ta’ala ya raya al'amarin albarkacin Imam Hussain (A.S) da jama'arsa. Saboda haka mutum zai ƙara gode wa Allah Maɗaukakin Sarki da wannan falala da wannan daraja da wannan zinariya da take hannun mutum da na wala’alla na nesa ke ganin ƙimarta” ya faɗa.

Daga ƙarshe Sheikh Yakub ya ƙarƙare maganarsa da cewa “Too muna fata Allah ya azirta mu da ziyararsu a nan duniya da cetonsu gobe ƙiyama. Muna fata Allah ya karɓi sa'ayinmu ya yafe kura-kuranmu. Allah ya ƙara wa Malam lafiya.

Wassalamu Alaikum WaRahmatullahi Ta'ala WaBarakatuhu”.

— Kalmomin Sheikh Yakub Yahya Katsina, a Maukibin Sheikh Zakzaky (H)...

Sheikhyakubyahyakatsina

ArbaeenKarbala / 1448 /2026

02Aug2026

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha