Daukar Fansa
-
Hujjatul Islam Sayyid Ali Khumaini: Tsayuwar Al'umma Ce Ta Kare Jamhuriyar Musulunci
Sayyid Ali Khumaini: Duk Wanda Yayi Tattaunawa Da Amurka Domin Yin Sulhu Maha'inci Ne + Bidiyo
Hujjatul Islam Sayyid Ali Khumaini ya jaddada cewa tsayuwar al'ummar Iran da goyon bayan da suka bai wa dakarun tsaro ne ya ba Jamhuriyar Musulunci damar shawo kan mawuyacin hali, yana mai cewa babban abin da Shahidin Jagora ya bari shi ne kare da kuma ƙarfafa akidar Juyin Juya Halin Musulunci.
-
Jagora: Mun Yi Alkawari Cewa Za Mu Ɗauki Fansar Jininka Mai Tsarki Da Jinin Dukkan Shahidai
Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamene'i ya fitar da saƙo inda ya yi godiya ta musamman ga halartar dubban miliyoyin al'ummar Iran da Iraki a jana'izar "Shahidin Iran", sannan ya ce wa Shahidin al'umma: "Mun yi alkawari cewa za mu ɗauki fansar jininka mai tsarki da jinin dukkan shahidan waɗannan yaƙe-yaƙe biyu a kan masu aikata wannan mummunan laifi marasa daraja. Wannan fansa ita ce buƙatar al'ummarmu, kuma babu shakka dole ne ta tabbata. Wadannan masu laifi, waɗanda aka san su tun daga manyansu har zuwa ƙananansu, za su tafi kabari tare da burin mutuwa cikin kwanciyar hankali wanda ba zai taɓa cika ba."
-
Jar Tutar Daukar Fansa, Al'ummar Musulunci Tana Jiran Wani Yunkurin Kamar Na Mukhtar
Tehran a yau ba wai kawai ta yi jana'izar jagoranta ba ne; Tehran a yau ta canja daga makoki zuwa yunkuri, daga zaman makoki zuwa ramuwa. Miliyoyin mutane, kai mu ce, miliyoyin tsaunuka masu aman wuta da suke tafarfasa waɗanda suke bubbugowa da zurfafan zukatansu suna masu shelenta neman fansar jini, sun mayar da titunan babban birnin zuwa tekun jajayen tutoci. Jajayen tutocin da ba iya alamar makoki su ke ba, har ma alamar guguwa ce da ke kan hanyar bayyana. Guguwa irin ta Mukhtar. Guguwa irin ta yunkuri. Guguwar da ta yi alkawarin kawar da girman kai na duniya. A yau Iran ba wai kawai ta raka jagora ba ne; a yau Iran, da jinin wanda ake zalunta, ta yi mubaya'a ga yaƙin maras aminci.