Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Bisa ga rahaoton tashar da ke da kusanci da fadar Elysee, Macron ya kuma umurci Firayim Minista Sebastien Lecornu da ya tura ƙungiyar gaggawa ta ma'aikatu, saboda yaɗuwar wutar.
Ministan harkokin cikin gida na Faransa Laurent Nunez ya a ranar Juma'a ya buƙaci Lecornu ya nemi taimakon sojoji don shiga cikin kashe gobara a yankin Gironde, inda wuta ta cinye hekta 14,000, wanda hakan ya sa aka kwashe mutane 110,000.
Faransa na fuskantar gobarar daji a kan yanayin zafin rani da ba a saba gani ba. Macron ya bayyana cewa ƙasar tana fuskantar wannan bazara da adadin gobarar daji mafi girma tun bayan yakin duniya na biyu.
A ƙarshen watan Yuni, hukumar kula da yanayi ta Faransa ta ɗaga matakin gargadin yanayi zuwa matsayi mafi girma saboda zafin rani a larduna 72 daga cikin 96, wanda hakan ya zama sabon tarihi. Zafin jiki ya kusa haura digiri 40, kuma ya haura shi a wasu yankuna.
…………………
Ra'ayinka