13 Yuli 2026 - 22:47
Source: ABNA24
Shekh Zakzaky: Akwai Haske Ga Mkaomar Gwagwarmaya + Hotuna

Taro Kan Gwagwarmaya A Iraq Jagora (H) ya kuma tabbatar da cewa, bisa ga yadda abubuwa ke tafiya, da farkawar matasa, hakan na nuna akwai haske a makomar Moqawamah a duniya gabadaya. Insha Allah.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Da yammacin yau Litinin, 28 ga Al-Muharram 1448 (13/07/2026), Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya halarci taro, wanda ƙungiyar da take wayar da kan al'umma game da fikirar Imam Khamne'i (RH), da ake kira "Lajnat Nida' Al-wali" suka shirya a birnin Bagadaza, Ƙasar Iraki, mai taken "Makomar Gwagwarmaya bayan Shahadar Imam Khamene'i (RH)".

A yayin da yake jawabi ga mahalartan, Jagora (H) ya ja hankalin ƴan Moqawamah akan muhimmancin haɗin kai, da tsayuwa ƙyam bisa tafarkin da Imam Khamene'i (QS) ya yi Shahada a kai.

Taro Kan Gwagwarmaya A Iraq Jagora (H) ya kuma tabbatar da cewa, bisa ga yadda abubuwa ke tafiya, da farkawar matasa, hakan na nuna akwai haske a makomar Moqawamah a duniya gabadaya. Insha Allah.

13/07/2026

28/Muharram/1448

Your Comment

You are replying to: .
captcha