Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Majiyoyin asibiti a zirin Gaza sun sanar da cewa, sakamakon hare-haren jirage mara matuki, na sama da manyan bindigogi na gwamnatin yahudawa a yankuna daban-daban na wannan ziri, a cikin awanni 24 da suka gabata, Falasdinawa 10 sun shahada wasu dada dama sun jikkata. Daga cikin waɗannan hare-haren, akwai hari a wani gidan zama a gabashin sansanin Al-Maghazi, da kuma tantunan 'yan gudun hijira a yankin Al-Qadisiyya a yammacin Khan Yunis, wanda ya haifar shahada da raunata.
Birnin Gaza a wannan lokaci ya sha mafi tsananin hare-hare; ta yadda jiragen yaƙi na gwamnatin yahudawa suka kai hari a wani wurin aikin ƙarfe da makamai masu linzami guda huɗu, wanda ya kai ga shahadar Falasdinawa huɗu. Haka kuma yankunan Al-Sabra, Al-Zaytun da Al-Shuja'iyya su ma sun fuskanci bama-bamai da harbin manyan bindigogi, wasu da dama sun jikkata. A cikin shahidan, akwai yarinyar Falasdinu mai shekaru 9 mai sunan "Tala Jum'a Abu Matar," wadda ta shahada sakamakon harbi kaitsaye daga sojojin yahudawa a sansanin Al-Nuseirat.
Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta sanar da cewa tun daga farkon tsagaita wuta zuwa yanzu, adadin shahidan sakamakon hare-haren gwamnatin yahudawa ya kai 1,100, kuma adadin raunata ya kai 3,546. Wannan ma'aikatar ta kuma sanar da cewa jimillar shahidan yaƙin Gaza tun daga 7 ga Oktoba 2023 zuwa yanzu ya kai 73,223, kuma adadin raunata ya kai 173,654.
……………………..
Your Comment