13 Yuli 2026 - 19:08
Source: ABNA24
Iran Ta Lalata Wuraren Amurka A Bahrain, Kuwait Da Jordan A Hare-haren Makamai Masu Linzami + Hotuna

Ofishin Hulda da Jama'a na Dakarun Juyin Musulunci na Iran ya ba da rahoton rubde cibiyar jagoranci da sarrafa jiragen mara matuki na Amurka a Bahrain, da tankokin man fetur da na’urar tsaron Patriot na Amurka a Kuwait, da kuma tankokin man fetur da ɗakin ajiyar alburusai na sansanin Prince Hassan na Jordan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Ofishin Hulda da Jama'a na Dakarun Juyin Musulunci na Iran ya ba da rahoton lalata cibiyar jagoranci da sarrafa jiragen mara matuki na sojojin Amurka a Bahrain, Jordan da Kuwait.

Dakarun Juyin Musulunci a cikin sanarwa daban-daban sun bayyana waɗannan hare-hare a matsayin martani mai ƙarfi na Iran ga munanan ayyukan baya-bayan nan na makiya Amurka a harin da suka kai wa cibiyoyi a lardunan kudu.

Sun kara da cewa: A matsayin martani ga waɗannan munanan ayyuka, mayakan sararin samaniya na dakarun juyin musulunci, a mataki na biyu na ayyukan ramuwar gayya, sun daddage muhimman cibiyoyin gyaran jirage masu saukar ungulu, wyraren ajiye jiragen yaƙi na P-8, da cibiyar jagoranci da sarrafa jiragen mara matuki na sojojin Amurka masu kashe yara a sansanin Amurka a Sheikh Isa na Bahrain.

Sanna dakarun sun lalata tankokin man fetur da na’urar tsaron sama na Patriot a sansanin Amurka a Ali Al-Salem na Kuwait, da kuma wata na'urar radar mai muhimmanci nau'in FPS a sansanin Ahmad Al-Jaber gaba daya.

Kuma Ayyukan ramuwar gayya suna ci gaba.

"Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, kuma zai tsayar da ƙafafunku."

Iran Ta Lalata Wuraren Amurka A Bahrain, Kuwait Da Jordan A Hare-haren Makamai Masu Linzami + Hotuna

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha