Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Shugaban kwamitin harkokin farar hula na majalisare Iran: An tsara wata doka mai cikakken bayani a kasar don kula da mashigar ruwa ta Hurmuz, wadda za a kammala nan ba da jimawa ba. A bisa wannan dokar, za a haramta jigilar kaya da jiragen ruwa da ke da alaƙa da gwamnatin Sahyuniya. Kasashen da ke yaƙar Iran ba za su iya wucewa ba tare da izinin Majalisar Tsaron Ƙasa ba. Haka kuma, ƙasashen da suka yi wa Iran barna ba za a bar su su ratsa mashigar ruwa ta Hormuz ba har sai sun biya diyya.
Sabbin bayanai game da shirin kula da mashigar ruwa ta Hormuz; daga hana wucewar jiragen ruwan Sahyoniya zuwa karɓar kuɗin shiga wanda biyansu zai kasance da Riyal a kuɗin ƙasar Iran.
Shugaban kwamitin harkokin farar hula na majalisar dokoki:
1. An haramta wucewar kowane irin jirgi ko kaya mallakar gwamnatin kama karya ta Sahyoniya a Mashigar Hurmuz gaba ɗaya.
2. An haramta wucewar jiragen ruwan ƙasashen da ke yaƙiar Iran bisa ga dokar.
3. An haramta wucewar jiragen ruwa ko kaya daga ƙasashen da ke ɗaukar matakai na ƙiyayya a kan fagagen Gwagwarmaya.
4. Za’a bar wasu jiragen ruwa su wuce idan sun sami izini kuma suka biya kuɗin "jagora, kulawa, da tsaro".
5. Biyan kuɗi zai askance da kuɗin ƙasar Iran (rial).
6. Duk wata ƙasa da ta shiga cikin yaƙin da aka ƙaƙabawa Iran za a bar ta ta wuce bayan ta biya diyya ga asarar da aka haifar a yakin.
7. Duk wata ƙasa ko mutum ko kungiya ko cibiya wanda ta sanya takunkumi na gefe ɗaya ga Iran ko kuma ya ɗauki wani mataki na ƙiyayya yana ƙarƙashin haramcin wucewa ta Mashigar Hormuz.
8. An hana wucewar jiragen ruwa na wata ƙasa da ke amfani da sunaye marasa tushe ga wanna mashigar sai ga kasashen da sukai anfani da suna mai inganci na “Tekun Farisa” a cikin takardu da bayanansu.
9. Za a kashe kuɗin da aka samu daga kuɗaɗen a wurare uku: ƙarfafa ƙarfin tsaron ƙasar da kuma rayuwar sojojin ƙasa; sake ginawa da haɓaka kayayyakin more rayuwa na ƙasar da kuma tabbatar da rayuwar Al’umma.
10. Rashin bin ƙa'idodin waɗannan dokoki zai haifar da kwace jirgin ruwan da ya aikata laifin da cin tara, da kwace kashi 20% na darajar kayan da yak e dauke da su.
Your Comment