7 Yuni 2026 - 08:02
Source: ABNA24
Hizbullah Ta kai hari Kan Taron Sojojin Isra’ila

Hizbullah tun daga safiyar wannan Asabar ta sanar da ayyuka 23 a kan sojojin yahudawa a Kudancin Lebanon, a lokacin da, baya ga kai hari ga wuraren taron sojojin mamaya, an kai wa motoci da tankokin Merkava da dama hari kai tsaye.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: A Sanarwar gwagwarmayar Musulunci (5): Mun kai wa taron motocin soji da sojojin makiya Isra'ila hari a gefen kudu maso gabashin garin Yahmar al-Shuqif da hare-haren rokoki da bindigogi

Dangane da hakan Hukumar Watsa Labarai ta Isra'ila daga sojojin mamaya na Isra'ila: Sojojin ajiya 4 sun jikkata sakamakon harin jirgin mara matuki mai fashewa a kudancin Lebanon.

Kafofin yada labaran Ibrananci sun ruwaito cewa wani soja na rukunin Egoz na sojojin wannan gwamnati ya mutu bayan mummunan raunin da ya samu a ranar Alhamis a Kudancin Lebanon. Wadannan kafofin yada labarai sun kara da cewa a ranar Juma'a an kashe wani sojan yahudawa daga bataliyar Givati a Kudancin Lebanon.

Shafin jarida na "Hadshut Bezman" shi ma ya buga cewa a yayin wani mummunan lamari na tsaro da ya faru a yau a Kudancin Lebanon, wasu sojoji 4 sun sami raunuka daban-daban.

Wadannan alkaluman asarar rayuka da raunin da sojojin yahudawa ke samu ana buga su ne, yayin da hukumar tantance labarai ta soja ta wannan gwamnati ke boye yawancin asarar rayuka da raunin da suke samu saboda tsoron rugujewar halin tunani na gida.

……………………………………..

Your Comment

You are replying to: .
captcha