4 Yuni 2026 - 14:00
Source: ABNA24
Ababil Na Hizbullah Ga Isra’ila: Mun Zo Amma Ba Mu Same Ku Ba

Gidan rediyon Isra'ila na "Kol Hai" ya yi irkrarin cewa "hadarin jirage masu sa ido a kudancin Lebanon yana kaiwa ga matakin fasaha tare da haifar da matukar damuwa a cibiyoyin tsaro da sojin Isra’ila”.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Gidan rediyon ya bayyana faifan bidiyon da Hizbullah ta fitar na ganuwar Shuqif a matsayin "na musamman".

Ya ce: "Bayan da Hizbullah ta fitar da wani faifan bidiyo na jirgin sa ido a saman katangar Shuqif, sojojin Isra'ila a karon farko sun yarda cewa suna da masaniya game da karfin hangen nesa na dare na ƙungiyar, kuma suna gudanar da bincike kan lamarin, tare da shaidun da wasu sojoji daga bataliyar Golani suka bayar game da wani jirgin sama mai fashewa da ya fashe kusa da su a cikin sa'o'in dare".

Hizbullah ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna wani jirgin sa ido na dare tare da daukar hoto bisa anfani da zafin jikin jirgin "Ababil" da ke kai hari a saman katangar ganuwar tarihi ta Shuqif da kewaye.

Bidiyon ya nuna cewa ganuwar ba sojojin Isra'ila a ciinta, bayan hakan kafafen yada labaran yakin sun yi sharhi suna masu cewa: "Mun zo amma ba mu same ku ba." Wannan yana nufin cewa maganar Isra'ila game da cikakken iko akan ganauwar da kuma kasanceware spjojinta a cikinta ba komai bane illa karya da farfaganda da tallata "wata nasara ta yaudara," wannan kuma yana nufin cewa gwagwarmayar Hizbullah ba ta barin Sojojin Isra’ila su zauna lafiya a ko'ina saboda ayyukanta da ke biyo baya da kuma irin hasarar da take yi mata.

……………………

Your Comment

You are replying to: .
captcha