Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Ofishin Ayatullahil Uzma Fayyad (R.A) a Najaf Ashraf, game da rasuwar wannan Marja’in koyi na musulmi a yau, bayan shafe shekaru yana fama da rashin lafiya, ya rasu yana da shekaru 96 a duniya, ya fitar da sako mai zuwa:
Bismillahir Rahmanir Rahim
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un
Tare da matuƙar bakin ciki, mun sami labarin rasuwar babban Marja’i, Ayatullahil-Uzma, Alhaji Shekh Muhammad Ishaq Fayyad (Allah ya tsarkake ruhinsa); babban mutum wanda ya shafe rayuwarsa mai albarka a hanyar bauta wa addini, koyar da ilimin Musulunci, tarbiyyar malamai da masana, da kuma yin ƙoƙari wajen yaɗa ilimin Ahlul-Bayt (a.s) da kuma bayyana hukunce-hukuncen shari'a mai tsarki.
Babu shakka, rasuwarsa, saboda matsayinsa mai girma na ilimi da addini, da kuma abubuwan da ya bari na gado na ilimi masu daraja, babban hasara ce ga makarantun addini da dukan muminai.
Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki da Ya saka shi cikin rahamarsa mai fadi da yalwa, kuma Ya haɗa shi da Muhammadu da iyalansa tsarkaka (Allah ya sanya albarkarsa ta tabbata a kansu baki ɗaya), kuma Ya bai wa waɗanda suka rage, almajiransa, mabiyansa da masoyansa haƙuri da natsuwar zuciya.
Za A Gudanar Da Jana'izar Gawarsa Mai Tsarki Kamar Haka:
- A Kazimain mai tsarki: Ranar Juma'a (19 ga Zul-Hajji 1447 AH) da karfe 9 na safe, daga Huseiniyar Al Yasin zuwa haramin Kazimain mai tsarki.
- A Karbala mai tsarki: Ranar Juma'a (19 ga Zul-Hajji 1447 AH) da karfe 5 na yamma, daga haramin Imam Husaini da ɗan'uwansa Abul Fadl al-Abbas (amincin Allah ya tabbata a gare su).
- A Najaf Ashraf: Ranar Asabar (20 ga Zul-Hajji 1447 AH) da karfe 9 na safe, daga gaban ofishinsa (Allah ya tsarkake ruhinsa) a Najaf Ashraf zuwa harami mai tsarki na Amirul Muminai.
Kuma Babu Wata Dabara Ko Ƙarfi Sai Da Ga Maɗaukaki Mai Girma.
Ofishin Ayatullahil-Uzma Alhaji Shekh Muhammad Ishaq Fayyad
Your Comment