Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: A Kudancin Lebanon, Gwagwarmayar Musulunci ta mayar da martani ga hare-haren Isra'ila tare da jerin ayyuka na rokoki da manyan bindigogi, da jirage marasa matuki na Ababil masu fashewa.
Hizbullah a yau Juma'a a cikin sanarwa masu yawa a jere ta sanar da cewa a Kudancin Lebanon ta aiwatar da jerin ayyuka a kan wuraren sojoji da kayan aikin gwamnatin yahudawa. In da ta bayyana cewa waɗannan ayyuka an yi su ne a kan take hakkin yarjejeniyar tsagaita wuta daga Isra'ila in da ta kai hare-hare a kan ƙauyukan Kudancin Lebanon - wanda ya haifar da shahadar wasu fararen hula da jikkatar wasu da dama.
A Cikin Sanarwar Yazo Cewa:
- Da karfe 00:30 na dare, sun kai wa wani taro na kayan aiki da sojojin Isra'ila a yankin "Al-Balu'" kusa da garin "Hadassa" hari da manyan bindigogi.
- Da karfe 01:45, sun kai wani taro na sojoji da kayan aikin Isra'ila a gabashin kudancin garin "Zutir Sharq" hari da rokoki.
- Da karfe 02:00, an sake kai wa wannan yanki hari da rokoki.
- Da karfe 03:15, an sake kai wani hari da rokoki a kan taron sojojin Isra'ila a gabashin kudancin "Zutir Sharq".
- Da karfe 03:20, sun kai wa taron sojojin Isra'ila a kudancin garin "Yahmar Al-Shuqif" hari da manyan bindigogi.
- Da karfe 03:45, an sake kai wa wannan yanki hari da rokoki.
- Tsakanin karfe 07:15 zuwa 07:30 na safe, sun kai wa taron sojoji da kayan aikin Isra'ila a gabashin kudancin "Zutir Sharq" hare-hare biyu da rokoki.
- Da karfe 12:20 na rana, sun kai wa wata motar sadarwa a mahaɗar "Al-Sal'ah" a garin "Al-Qantar" hari da jirgin mara matuki na "Ababil" mai fashewa kuma motar ta kama da wuta.
- Da karfe 12:50, sun kai wa wata motar soji ta "Nemara" a wannan yanki hari da jirgin mara matuki na kunar bakin wake kuma ta lalace.
- Da karfe 13:10, sun kai wa taron kayan aiki da sojojin Isra'ila a kewayen ganuwar tarihi ta "Al-Shuqif" hari da rokoki.
A lokaci guda, kafofin yada labaran Isra'ila sun sanar da cewa wani jirgin soji mai saukar ungulu ya sauka a asibitin "Tel Hashomer" kuma wannan jirgin yana dauke ne da sojojin da suka jikkata zuwa asibitin.
Haka kuma, Gwarwarmayar Lebanon ta wallafa hotunan aikin da aka yi a ranar 1 ga Yuni, 2026, wanda aka kai wa taron kayan aikin sojojin Isra'ila a kewayen kudancin garin "Al-Adaisah" a Kudancin Lebanon hari da ruwan rokoki.
A lokaci guda, Hizbullah ta Lebanon ta wallafa bidiyon aikinta a ranar 1 ga Yuni, 2026, wanda aka kai wa tankar "Merkava" ta sojojin Isra'ila a kewayen kudancin garin "Yahmar Al-Shuqif" a Kudancin Lebanon hari da jirage mara matuki na "Ababil" masu fashewa.
Your Comment