A ranar juma'a 5 ga wata Yuni 2026, ɗaliban Fodiyya na Harkar Musulunci ƙarƙashin jagoranci Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), da ke garin Karaba, sun gudanar da walimar Idin Ghadeer a muhalli Fudiyya Karaba, a ƙaramar hukumar Kubau jihar Kaduna.
Bayan buɗe taro da Addu'a, sai aka saurari karatun Alkur'ani mai girma daga bakin Fatima Adam, sai kuma (Quiz) a kan Imam Ali (A.S). Malam Adamu Abubakar ne ya gabatar da jawabi, dangane da batun da ya shafi Ghadeer.
Bayan kammala jawabi anyi addu'a aka sallami kowa.
Rahoto Daga: Al'amin Zakariyya Karaba
Zaria Media Forum
Your Comment