8 Afirilu 2026 - 06:17
Source: ABNA24
Cikakkun Bayanai Kan Shiri 10 Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Gabatar Akan Akan Tsawaita Wuta

Cikakkun bayanan sharudda 10 da aka gabatar daga bangaren Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wadanda ta amince da su a matsayin tushen yarjejeniyar tsagaita wuta, sune dalla-dalla.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wannan shirin, wanda ke kayyade tsarin karshe na dakatar da rikice-rikice, ya hada da tanade-tanade wadanda sune muhimman tushe kamar haka:

1- Cikakken dakatar da duk wani keta iyaka ga Iran da kungiyoyin gwagwarmaya. 

2- Ficewar sojojin Amurka daga yankin, da hana duk wani hari daga sansanoni kan Iran, da kuma nisantar duk wani abu da ake nuna shirye-shiryen yaki.

3- Takaita wucewa ta yau da kullum a mashigar Hormuz ga jiragen ruwa na tsawon makonni biyu, a matsayin amintaccen ƙa'idar nassin shirin wanda ke ƙarƙashin kulawa da dokokin wannan ƙasa. 

4- Dage duk wasu ƙananan da manyan takunkumi da na Majalisar Dinkin Duniya. 

5- Samar da yadda za'a biya asarar da aka wa Iran ta hanyar samar da asusun zuba jari na kudi. 

6- Iran ta ɗauki alƙawarin ba zata ƙera makamin nukiliya ba. 

7- Yarda da 'yancin Iran na samar da wadataccen sinadarai da yin tattaunawa akan gwargwadon yadda zata tanada. 8- Iran ta amince da yin tattaunawa kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin kasashen biyu da kasashen yankin don muradunta. 

9- Tabbatar da rashin keta iyaka ga duk masu zalunci a kan duk kungiyoyin gwagwarmaya. 

10- Kawo karshen dukkan kudurori na kwamitin gwamnoni da kwamitin tsaro da kuma amincewa da zartarwa a cikin kudurin Majalisar Dinkin Duniya. 

Majiyar da aka sanar ta jaddada cewa, a baya Iran ta yi watsi da shirin Amurka mai matakai 15, inda ta yi watsi da shawarar Amurka da ta yi na dakatar da buɗe wuta har sai idan Amurka ta amince da shawarar da Iran ta fitar tare da sanar da yarjejeniyar ta bangare Trumpa hukumance kan shirin, wanda Trump a hukumance ya amince da shirin Iran na mataki goma.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha