Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Karɓar takardun shaidar "Simon Sirocy" sabon jakadan gwamnatin yahudawa a Burkina Faso daga Kyaftin "Ibrahim Traore" shugaban gwamnatin rikon kwarya ta Burkina Faso, ya faru ne a wani lokaci mai muhimmanci na siyasa da tsaro. Lokacin da Traore ya fara gagarumin yaki da cibiyoyi da shugabannin Musulunci, a ƙarƙashin taken yaƙi da Musulunci mai tsattsauran ra'ayi.
Dangane da rahoton gidan talabijin na Al Jazeera, ko da yake babu wata hujja a fili da ke danganta waɗannan matakai guda biyu, amma wannan naɗin yana nuna haɗin kai mai zurfi tsakanin buƙatar Burkina Faso na sabon abokin tsaro, da ƙoƙarin gwamnatin yahudawa na faɗaɗa tasirinta a yankin Sahel na Afirka.

Naɗin Da Aka Yi Cikin Shirin Makarkashiya
Kwamitin naɗi na ma'aikatar harkokin waje ta gwamnatin yahudawa, ya zaɓi Simon Sirocy a matsayin jakadan wannan gwamnati a kasashe huɗu na Afirka waɗanda suka haɗa da Côte d'Ivoire, Burkina Faso, Benin da Togo.
"Itamar Eichner" ɗan jaridan diflomasiyya na jaridar Ibrananci "Yedioth Aharonoth," ya ba da rahoton cewa, an yi wannan naɗin ne a cikin jerin naɗaɗɗen da kwamitin da "Gideon Sa'ar" ministan harkokin waje na gwamnatin yahudawa ke shugabanta ya amince da su, kuma an shirya gabatar da su ga hukumar wannan gwamnati don amincewa ta ƙarshe.
Sirocy ba ya zaune a birnin "Ouagadougou" babban birnin Burkina Faso, ya kafa ofishinsa a ofishin jakadancin gwamnatin yahudawa a birnin "Abidjan" babban birnin Côte d'Ivoire. Bayanan aikin sa na hukuma sun nuna cewa wannan jami'in diflomasiyya ya shiga ma'aikatar harkokin waje ta gwamnatin yahudawa a shekara ta 2018, kuma a baya ya yi aiki a matsayin mataimakin jakadan wannan gwamnati a Kamaru, kuma mai kula da batutuwan diflomasiyya, tattalin arziki da al'adu. Ya kuma yi aiki a fannin haɓaka kasuwancin noma da kasuwanci, da kuma nazarin rikice-rikicen Afirka.
Waɗannan bayanan sun sa Sirocy ya dace da tsarin da gwamnatin yahudawa ke bi. Tsarin da a gefe guda yake bin fannoni kamar noma, ruwa da fasaha, kuma a gefe guda yana mai da hankali kan batutuwan tsaro da sanin rikice-rikicen gida. Don haka, ba ya zama ace zaɓar kamar Sirocy ga Burkina Faso ya zamo shawara ce ta gudanarwa kawai ba, a'a, wani ɓangare ne na ƙoƙarin samar da kasancewa sassauƙa a yammacin Afirka da yankin Sahel.
Samun Dacewar Lokaci Mai Muhimmanci
Gabatar da takardun shaidar sabon jakadan gwamnatin yahudawa ya zo daidai da ƙaruwar yaƙin Traore a kan cibiyoyin Musulunci. Dangane da rahoton da gidan talabijin na Al Jazeera ya buga a ranar 21 ga Yuli 2026, Traore ya bayyana cewa abin da ake kira Musulunci mai tsattsauran ra'ayi, ba shi da wuri a ƙasar, kuma ya yi barazana ga malaman addini da ya kira masu tsattsauran ra'ayi, ya ce an fara yaƙin.
Ya kuma yi barazanar dakatar da ayyukan limaman da, a cewar jami'an gwamnati, ke amfani da hudubunsu don yaɗa saƙonnin tsattsauran ra'ayi.
Gwamnatin rikon kwarya ta Burkina Faso ta kuma amince da sabuwar doka game da 'yancin addini, wadda a cewar jami'an wannan ƙasa, manufarta ita ce tabbatar da rabuwar addini da gwamnati, da kuma ƙara sa ido kan albarkatun kuɗi da batutuwan addini. Kafin haka, an kama wasu limamai da yawa, kuma bayan zanga-zangar da ta buƙaci 'yantar da "Mohammed Ishaq Kindo" limamin juma'a, an rufe babban masallacin Ahlus-Sunnah a birnin Ouagadougou.
Traore ya kuma ba da labarin wani shiri na dawo da ɗaliban da ke karatu a ƙasashen Larabawa a fannonin ilimin addini, kuma ya yi iƙirarin cewa kusan ɗalibai 800,000 ne ke karatun ilimin Musulunci a ƙasashen waje, ba tare da samun ƙwarewar sana'a ba.
Ya har ma ya yi magana game da yiwuwar ɗaukar matakai game da zama ɗan ƙasa a kan waɗanda suka ƙi komawa Burkina Faso. Matakin da ke nuna cewa fuskantar gwamnati ba ta tsaya ga kula da mimbari kawai ba, a'a, tana neman sake fasalin yanayin addini da ilimi na ƙasar.
Matsalar Tsaro
Mummunan yanayin tsaro a Burkina Faso, ya bayyana ƙarancin fuskar da Traore ke ƙoƙarin nunawa game da ikonsa na dawo da iko a kan ƙasar. "Zeev Avrahami" marubuci a cikin wata makala da aka buga a "Yedioth Aharonoth," ya bayyana Burkina Faso a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe mafi haɗari a duniya, kuma ya ce ƙungiyoyi masu alaƙa da ISIL da Al-Qaida suna iko da cikakkun yankuna na wannan ƙasa.
A rubutun wannan marubuci, Traore ya gina wa kansa fuska ta mai ceton Afirka, kuma tare da dogaro da batun adawa da kasashen yamma da yin farfaganda mai yawa, ya ƙarfafa wannan fuskar. Yayin da ta'addanci ke ci gaba da faɗaɗa, kuma alamun rayuwar dimokuradiyya a Burkina Faso sun ragu.
Wannan ra'ayi ya dace da nazarin jaridar Ibrananci "Calcalist." Wannan jaridar ta yi magana game da babban yaƙin neman zaɓe na talla a sararin dijital, wanda ke amfani da Na’urar wucin gadi, yana ƙoƙarin nuna Traore a matsayin shugaba mai juyin juya hali. A daidai lokacin da ayyukansa a kan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ba su kai ga sakamakon da ya yi alkawari ba.
Traore tun daga lokacin da ya hau mulki, yana neman madadin Faransa wajen yaƙi da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai. Gidan talabijin na 12 na gwamnatin yahudawa ya ba da rahoton cewa, Traore a lokuta da dama ya bayyana sha'awar ƙasarsa na amfani da wani bangare wajen yaƙi da ta'addanci bayan ƙarshen kasancewar sojojin Faransa.
Da farko ya karkata zuwa ga Rasha, amma ci gaba da mummunan yanayin tsaro ya sa bambanta abokan huldar waje ya zama larura.

Gwamnatin Yahudawa A Matsayin Ƙofar Shiga
Dangane da ra'ayin Cibiyar Nazarin Tsaro ta Ƙasa ta gwamnatin yahudawa, a nan ne darajar Isra'ila ga Ouagadougou ta bayyana. Wannan cibiya ta yi imanin cewa, bangaren tsaro a cikin shekaru goma da suka gabata ya zama muhimmin bangare a dangantakar gwamnatin yahudawa da kasashen Afirka; har ma a lokuta da dangantaka ta fara da batutuwa masu zaman kansu kamar noma, ruwa da lafiya.
"Yaron Salman" mai bincike na wannan cibiya, ya ce gwamnatin yahudawa ta yi amfani da horon soji, bayar da kayan aiki, da samar da ƙarfin leken asiri da fasaha don ƙarfafa kasancewarta a ƙasashen da ke fuskantar ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
Nazarorin yahudawa kuma suna ɗaukar faɗaɗa ƙungiyoyin jihadi a Afirka a matsayin dama don haɓaka haɗin gwiwa da gwamnatocin gida.
A cikin wani bincike na baya-bayan nan game da gasar duniya a Afirka, "Denis Citrinovich" masanin tsaro na Cibiyar Nazarin Tsaro ta Ƙasa ta gwamnatin yahudawa, ya sanya Burkina Faso a cikin kasashen da suka zama fagen tasirin Rasha. Yayin da rawar Turkiyya da Iran ma ke faɗaɗa a wannan yanki.
A cewar wannan masani, jimillar waɗannan abubuwan gasa suna tura gwamnatin yahudawa zuwa neman ƙafa a ƙasashen yankin Sahel na Afirka, ba wai kawai don fuskantar ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ba, a'a, don sa ido kan abokan hamayyarta, da kuma samar da sabbin hanyoyin dangantakar tsaro da diflomasiyya.
Dangantaka Mai Yiwuwa
A cikin rahoton da gidan talabijin na Al Jazeera ya buga, an ce an dakatar da karɓar takardun shaidar jakadan gwamnatin yahudawa tun daga lokacin rani na 2025, kuma a ƙarshe an amince da shi ba tare da hayaniya ba. Maraba da sabon jakadan a fili ta haka, ya kawo ƙarshen lokacin taka tsantsan da fuskar adawar yamma da Traore ya sanya wa dangantakar.
Wannan rahoto ya kuma danganta wannan mataki da sha'awar kasashen membobin ƙungiyar kasashen Sahel ga fasahohin tsaro na Isra'ila.
Duk da haka, babu wata takarda ta Isra'ila ko Burkina Faso da ke ba da labarin wata yarjejeniya ta tsaro ko leken asiri tsakanin bangarorin biyu. Haka kuma babu wata hujja da ke nuna cewa yaƙin Traore a kan cibiyoyin Musulunci ya fara ne tare da haɗin kai da Tel Aviv.
Abin da ake gani a yanzu, ya fi kama da haɗin kai na siyasa. Traore yana buƙatar fasahohi da ƙwarewar da zai iya amfani da su wajen fuskantar abokan hamayyarsa masu ɗauke da makamai, da kuma ƙarfafa ikonsa na cikin gida. A gefe guda, gwamnatin yahudawa na neman sabon abokin aiki a yankin da tasirin manyan ƙasashen yamma ke raguwa, kuma Rasha, Iran da Turkiyya ke fafatawa don ƙarin tasiri.
A Takaitace
A takaice, naɗin Simon Sirocy ba ya zama kamar nufin samar da sabuwar dangantaka ba, a'a, ya fi nuna haɓaka matakin sadarwa da bayyana shi.
Daidaitawar wannan naɗin da yaƙin Traore a kan abin da ake kira Musulunci mai tsattsauran ra'ayi, yana ba wannan kusanci fannonin tsaro, amma shi kaɗai baya tabbatar da wanzuwar kawance na hukuma da aka bayyana.
Abin da ke tabbata shi ne, rashin nasarar zaɓuɓɓukan Faransa da Rasha wajen kawo ƙarshen tayar da kayar baya, ya sa Traore ya karkata zuwa ga bambanta abokan huldar waje. Yayin da rikicin da ake ciki, ya ba gwamnatin yahudawa dama ta shiga ta ƙofar tsaro da fasaha, kuma a lokaci guda, ta ciyar da dangantakarta a ƙarƙashin sunan haɗin gwiwar noma, ci gaba da tattalin arziki.
………………….
Ra'ayinka