27 Yuli 2026 - 08:39
Source: ABNA24
Haramin Sayyid Abbas Ya Buɗe Mawkibin Al'adu na Baiɗaya A Cikin Rukunin Ummul-Baneen Domin Hidimatawa Masu Ziyara + Hotuna

Haramin Al-Abbas (a.s) mai tsarki ya buɗe Maukibin al'adu na Baiɗaya a kan hanyar mahalarta ziyara a kan titin (Karbala - Najaf), a cikin rukunin Ummul-Baneen (amincin Allah ya tabbata a gare ta) domin hidimawa mahalarta ziyara, a daidai lokacin da mahalarta ziyara ke kwararowa don tunawa da Ziyarar Arba'in.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Haramin Al-Abbas (a.s) mai tsarki ya buɗe Maukibin al'adu na Baiɗaya a kan hanyar mahalarta ziyara a kan titin (Karbala - Najaf), a cikin rukunin Ummul-Baneen (amincin Allah ya tabbata a gare ta) domin hidimawa mahalarta ziyara, a daidai lokacin da mahalarta ziyara ke kwararowa don tunawa da Ziyarar Arba'in.

Taron buɗewar ya sami halartar wani memba na kwamitin gudanarwa na Harami Mai Tsarki, Dokta Abbas Al-Dadah Al-Moussawi, da wasu dama daga cikin jami'anta, masana addini da ilimi, da kuma gungun mahalarta ziyara. An fara ne da karatun wasu ayoyi daga Alqur'ani Mai Tsarki, sannan aka yi jawabi daga Harami Mai Tsarki wanda Malam Ahmed Sadiq, shugaban Gidauniyar Al-Wafi ta Rubuce-rubuce da Nazari kuma mai kula da Maukibin, ya gabatar, inda ya bayyana yanayin Maukibin da kuma wuraren al'adu daban-daban da shirye-shiryen da ya ƙunsa.

Sadiq ya ce: Haramin Al-Abbas (a.s) mai tsarki ya buɗe Maukibin al'adu na Baiɗaya a kan hanyar mahalarta ziyara a Titin (Karbala - Najaf), kuma za a kuma buɗe shi a titunan (Baghdad - Karbala) da (Babil - Karbala), yana bayyana cewa wannan aikin ya zo ne a cikin ayyukan harami mai tsarki na kafa tushen yunkurin Imam Husain (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da kuma amfani da yanayin Ziyarar Arba'in don yada wayewar addini da al'adu tsakanin mahalarta ziyara.

Ya kara da cewa ana gudanar da Maukibin ne tare da halartar sassan kusan tara na Haramin Al-Abbas (a.s) mai tsarki, waɗanda suka haɗa ƙarfinsu don gabatar da wani shiri na al'adu na gaba daya wanda ya haɗa da ayyuka iri-iri na tunani, akida, da wayar da kai waɗanda ke nufin ɓangarori daban-daban na mahalarta ziyara, musamman matasa, da nufin inganta wayar da kan al'adun Imam Husain (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da faɗaɗa fahimtar akida.

A nasa bangaren, shugaban Sashen Ci Gaba Mai Dorewa a Haramin Al-Abbas (a.s) mai tsarki, Dokta Muhammad Hassan Jaber, ya ce buɗe Maukibin al'adu na Baiɗaya ya zo daidai da ƙaruwar yawan mahalarta ziyarar Arba'in na Imam Husain (amincin Allah ya tabbata a gare shi), yana mai ishara cewa shi ne Maukibin al'adu na farko da aka buɗe a Titin Najaf-Karbala, kuma za a buɗe a sauran wasu titunan.

Jaber ya bayyana cewa mawkibobin al'adu da Haramin Al-Abbas (a.s) mai tsarki ya buɗe suna da nufin haɓaka fannonin tunani da al'adu na mahalarta ziyarar Arba'in, bisa ga cewa yunkurin Imam Husain (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana wakiltar aikin gyara da ke mayar da hankali kan gina wayar da kan akan waye Imam Husain As. Ana cimma wannan ta hanyar shirye-shiryen da ke bayyana manufofin yunkurin Imam Husain da sakonsa na ɗan'adam da gyara, wanda ke ba da gudummawa wajen yaɗa tunaninsa zuwa ɓangarori daban-daban na al'umma.

………….

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha