Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Majiyoyin Labarai sun nuna cewa an ga tashin jirage mara matuki da harba makamai masu linzami daga Yemen zuwa Saudiyya Arabiya.
Wanda Rahotanni sun nuna cewa an ji karar fashe-fashe da dama a Jizan na Saudiyya. Sannan Fashe-fashe masu ƙarfi sun girgiza birnin tashar jiragen ruwa na "Yanbu" na Saudiyya.
Kafofin Yada Labarai Na Larabawa sun ba da rahoton cewa ɗaya daga cikin muhimman cibiyoyin Saudiyya a Jizan ya fuskanci harin makami mai linzami na Yemen. Sanna an jiyo fashe-fashe a Sansanin Sojan Sama na "Khamis Mushait" na Saudiyya. Kafofin Yada Labarai Na Larabawa: Biyo bayan hare-haren makamai masu linzami a kan Saudiyya, an katse wutar lantarki a yankuna daban-daban na birnin Jizan na wannan ƙasa.
Rahotanni sun ba da labarin fashe-fashe masu ƙarfi a birnin "Damad" na Saudiyya. Kafofin Yada Labarai Na Larabawa: Makamai masu linzami na Yemen sun kuma kai hari a yankin "Hayy al-Matar" kusa da filin jirgin sama na Abdullah na Saudiyya.
Cibiyoyin sa ido na jiragen sama sun ba da rahoton samun cikas a zirga-zirgar jiragen sama, da rashin yiwuwar saukar wasu jiragen sama a filayen jiragen sama na kudancin Saudiyya.
In da Filayen jiragen sama na "Amir Abdul Mohsen bin Abdul Aziz" da "Abdullah bin Abdul Aziz" a Jizan da Yanbu, biyo bayan hare-haren Yemen, sun dakatar da ayyukansu na ɗan lokaci. Filayen Jiragen Sama na Jeddah da Riyadh sun dakatar da jiragen su bayan harin Yemen a kan birnin Jizan na Saudiyya.
Majiyoyin Yemen: Tsananin harin Yemen a kan Saudiyya, yana kama da hare-haren Iran a kan sansanonin Amurka a yankin.
Martanin Yamen Bayan Harin: Nasrallah Amer, memba na Majalisar Koli ta Siyasa ta Ansarallah:Ku manta da girman da matakin hare-haren da suka gabata daga ƙwaƙwalwarku; yanayin a wannan karon ya bambanta gaba ɗaya.
Gabanin Harin: Hukumar Tsaron Jama'a ta Saudiyya: An ƙaddamar da faɗakarwa daga dandalin faɗakarwa na ƙasa a lardin Yanbu don gargadi game da haɗari.
Kafofin yada labarai na Saudiyya sun yi magana game da tashin gobara da fashe-fashe a yankunan kudancin Masarautar.
………………..
Ra'ayinka