Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kafofin yada labaran Isra'ila sun ba da rahoton cewa sojojin Isra'ila 6 ne suka jikkata a wani hari da da Hizbullah ta kai garin Deir al-Assad da ke arewacin Falasdinu.
Hizbullah ta kai hari kan gungun sojojin Sahayoniyya a kusa da yankin sojin Al-Marj da ke gaban garin Meika da ke kan iyakar Meika.
Sannan Hizbullah Lebanon ta sanar da cewa, a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, dakarunta sun gudanar da ayyuka 34 a yankunan kan iyaka da ke da zurfin kilomita 20 a Falasdinu da aka mamaye.
Majiyoyin labarai sun ba da rahoton wani sabon harin makami mai linzami na kungiyar Hizbullah da ta kai wa Jalil a arewacin Falasdinu.
A wani rahoton kuma sama da dala biliyan 15 asarar da ta hau kan gwamnatin sahyoniyawa ta a yakin da Iran da Hizbullah suka yi.
Wanda asarar yakin da ake yi da Iran da Hizbullah a Isra'ila ya karu zuwa kusan dala biliyan 15, kuma wannan adadi zai karu a nan gaba yayin da rikicin ke ci gaba da fadada sakamakon tattalin arzikinta.
Ma'aikatar yaki ta Isra'ila ta nemi kusan dala biliyan 12.4 don biyan kudaden kayayyakin soji. Kuma kimanin adadin neman diyya 26,000 ne aka shigar da su don neman diyya sakamakon asarar da harin makami mai linzami na Iran ya haifar a Isra'ila, wanda ƙimar kuɗin za ta kai dala miliyan 320 zuwa dala miliyan 450. Hizbullah ta kona wasu tankunan yaki guda biyu na Merkava tare da kai harin manyan bindigu a kan tudu a birnin Einata.
Hizbullah Lebanon ta aiwatar da ayyukan kai hare-hare 61 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata. Dakarun Musulunci na Lebanon sun lalata tankokin yaki guda biyar da manyan bindigogi guda biyu bayan sun harba rokoki da manyan hare-haren jiragen sama marasa matuki.
Your Comment