22 Maris 2026 - 13:32
Source: ABNA24
Iran Ta Kai Munanan Hare-Hare Kan Cibiyar Nokiliya Dimona Da Arad

Babbar Cibiyar Hafsan Hafsoshin ta ba da umarnin ci gaba da gudanar da bincike kan gazawar tsaron sama wajen dakile makamai masu linzami a Dimona da Arad.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Adadin wadanda suka jikkata a harin makami mai linzami da Iran ta kai kan Falasdinu da aka mamaye ya kai zuwa mutane 175 a jaridar Yediot Ahronoth ta ba da rahoton cewa, adadin wadanda Iran ta kai hari a daren jiya kan "Arad" da "Dimona" a yankunan da aka mamaye sun karu zuwa 175. Sannan harin ya haifar da barna da rugujewar gininnika masu yawa a wurin da aka kai harin makami mai linzami na Iran a Dimona gwamnatin sahyoniyawan ta bukaci mazauna yankin da makamin ya afkawa Dimona da su bar gidajensu.

A daidai lokacin ne kuma wani makami mai linzami kai tsaye ya afkawa yankin Arad da ke kudancin Isra'ila

Majiyoyin Ibrananci sun bayar da rahoton cewa: Iran da alama ta yi nasarar rage karfin tsarin tsaron kariya a kudancin Isra'ila kamar yadda ta yi alkawari.

Bayan harin a kidayar farko sahayoniya 30 sun jikkata a Arad. Amma daga baya adadin wadanda suka jikkata a Arad ya karu zuwa mutane 60.

Ɗan jaridar canal 13 na Isra'ila ya bayar da rahoton cewa lamarin harin yayi tsanani da tsamari sosai sannan an kai sahayoniyawan da suka jikkata zuwa cibiyoyin kiwon lafiya.

Ba jima ba kuma an samu karin adadin wadanda suka jikkata sama da 100.

Shaidun gani da ido sun ce a harin makami masu linzami na Iran kan Dimona Da Arad Mutane da dama ne suka mutu tare da raunata. Shaidu na yankin sun bayar da rahoton cewa mutane da dama ne suka mutu sannan sama da 100 suka jikkata, yayin da majiyoyin hukuma suka bayyana cewa 50 kawai suka jikkata.

Jami'an tsaron Isra'ila sun hana daukar hotuna tare da fitar da karin bayani. Akalla mutane 20 ne suka mutu sannan sama da 200 suka jikkata kamar yadda kafafen yada labaran Isra'ila suka faɗa a birnin Arad.

Tashar ta 14 ta kuma yi ikirarin cewa makamin na Iran da aka harba a birnin Arad yana da kilogiram 450 na kan yaki. A cewar cibiyar sadarwar, yunkurin tsaro kariyar sama guda biyu na kai hari ga makamin da nufin kaɗe shi ya ci tura.

Netanyahu: Muna cikin dare mai wahala. Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, a matsayin martani ga harin makami mai linzami na Iran a kudancin yankunan da aka mamaye, ya sanar da cewa, gwamnatin na cikin dare mai matukar wahala a yanayin yakin da ake yi na makomar "Isra'ila" Arad.

Kakakin Sojojin Isra'ila: Makamin da aka yi amfani da shi a harin da aka kai Arad ya kasance sabon abu ko kuma ya bambanta da sauran makaman. Sakamakon wannan harin, unguwa gaba ɗaya ta lalace.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha