20 Nuwamba 2025 - 16:53
Source: Almanar
Isra'ila Ta Yi Amfani Da Munanan Makaman Da Aka Haramta A Kudancin Lebanon

The Guardian ta bayyana cewa "hotunan ragowar baraguzan makamai a kudancin Lebanon sun nuna cewa Isra'ila ta yi amfani sosai da makamai masu guba na rukuni da aka haramta a yakin da ta yi na kwanan nan da Lebanon."

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Hotunan, wadanda kwararru shida na makamai daban-daban suka yi nazari a kansu, sun nuna ragowar sabbin makamai rukuni guda biyu na Isra'ila da aka samu a wurare uku daban-daban a kudancin Kogin Litani: a kwarin Zibqin, Barghez da Deir Siryan.

Isra'ila Ta Yi Amfani Da Munanan Makaman Da Aka Haramta A Kudancin Lebanon

Shaidar ita ce alama ta farko da 'yan mamaye Isra'ila suka yi amfani da makaman rukuni tun bayan yakin 2006 da Lebanon kuma karo na farko da aka tabbatar da cewa sun yi amfani da sabbin nau'ikan guda biyu da aka samu: harsashin makamin Barak Eitan M999 155mm da rokoki na Ram Eitan 227mm.

Isra'ila Ta Yi Amfani Da Munanan Makaman Da Aka Haramta A Kudancin Lebanon

A cewar jaridar, "Kasashe 124 shiga Yarjejeniyar Kan hana anfani da Rukunin makaman zuwa yanzu Rukunin, wanda ya haramta amfani da su, samarwa da canja wurin su, yayin da Isra'ila ba ta daga cikinsu amma tana amfani da su."

Tamar Gabelnik, darektan yarjeniyar yaƙi da makami ta Cluster Munitions, ta ce amfani da waɗannan makaman "koyaushe ya saɓa wa dokar wajibcin girmama dokokin jin kai na duniya," tana mai cewa "ba sa bambanta tsakanin fararen hula da mayaka kuma suna ci gaba da zama masu kashewa a tsawon shekaru da dama".

Your Comment

You are replying to: .
captcha