Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: An gudanar da wani taron na tunawa da ranar shahadar Sayyida Fatima Zahra (A.S) a Tehran a ranar Litinin, wanda ya kunshi jawabi mai muhimmanci daga Malama Zeinatudden Ibrahim, matar Sheikh Ibrahim Zakzaky - shugaban Harkar Musulunci a Najeriya.
An shirya taron, wanda aka shirya a Jami'ar Shahed kuma malamai, daliban makarantar hauza, da malamai suka halarta, tare da daukaar nauyin Cibiyar Al-Basira ta Najeriya da kuma kungiyar dalibai bias koyarwar Sheikh Zakzaky H. Taron ya fara ne da karatun Alkur'ani Mai Tsarki, sannan sai Ziyarat Ashura, Addu'a Tawassul, Ziyarar Sayyida Zahra (A.S), da kuma wakokin bege da girmama Ahlul Bayt (As).
Da take jawabi a wurin taron, Malama Zeinat —wanda aka fi sani da “Uwar Shahidai” saboda shahadar 'ya'yanta shida a gwagwarmayar—ta jaddada muhimmancin ruhaniya da siyasa na tunawa da zaluncin da sayyidah Fatima (AS) ta fuskanta. Ta jaddada cewa dole ne a yi jimami tare da jajircewa kan ka'idodin da wannan baiwar Allah mai tsarki ta tsaya a kansu.
“Bai isa a yi bakin ciki kan bala'o'in da suka faru da Sayyadah Zahra (AS) ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne kare gaskiyar da ta sadaukar da kanta a kanshi,” in ji ta. “Mutumin da bai halartar tarukan makoki amma yana fito na fito da zalunci zai iya samun daraja fiye da wanda ya ke zuwa amma yana daidaita kansa da azzalumai.”
Ta danganta rikicin da ke fuskantar al'ummar Musulunci a yanzu da juya baya da ya faru bayan rasuwar Manzon Allah (AS). Ta ce: “Da mutane sun amince da wasiyyar Annabi, da duniyar Musulmi ba za ta sha wahala da waɗannan bala'o'in ba a yau ba”.
Ta yi martini ga zargin da ake yi na cewa Sayyidah Zahra (AS) tana nemen ikon duniya ne, inda Malama ta jaddada cewa tsayawarta kyam kawai ta kasance bisa ga biyayya ga umarnin Allah ne. "Mumini wanda ya fahimci nauyin shugabanci ba ya son gwamnati don samun wata riba ta kashin kansa. Sayyidah Zahra (AS) ta tsayu ne don cika umarnin Annabi, ba don neman abin duniya ba".
Ta yi wa ɗaliban da suka halarci taron jawabi, ta roƙe su da su sadaukar da karatunsu ga hidima wa Musulunci a ƙarƙashin jagorancin Sheikh Zakzaky. Ta kuma yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi na guje wa fuskantar cikin rashin adalci. Da cewa: "Wasu suna cewa ba lokaci ne na gwagwarmaya ba kuma ya kamata mu yaɗa Shi'anci kawai. Amma menene anfanin Shi'anci ba tare da gwagwarmaya da zalunci da bin umarnin Allah ba?".
Malama Zenat ta kammala da bayyana fata da tabbacin makomar Musulunci a Najeriya. Ta bayyana cewa: "Wannan addini zai tabbata a Najeriya," "Babu wani iko - Amurka, ko Isra'ila, ko Japan - da zai iya dakatar da shi".
Taron ya kuma ƙunshi jawabai daga Sheikh Muhammed Sani Malafa da Abdullahi Ahmed Fudiya. Mahalarta taron sun haɗa da ɗalibai daga Makarantun Kum da jami'o'i da dama. Taron ya ƙare da yin addu'a.
Your Comment