Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud ya karɓi saƙon rubutun wasika daga Shugaban Iran Masoud Pezzekian a ranar Litinin.
A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya (SPA), an isar da saƙon ga ɓangaren Saudiyya a lokacin wani taro tsakanin Alireza Rashidian, shugaban ƙungiyar Hajji da ziyara ta Iran, da Abdulaziz bin Saud bin Nayef bin Abdulaziz, Ministan Harkokin Cikin Gida na Saudiyya.
A lokacin taron, ɓangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi juna. Alireza Enayati, jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Saudiyya, shi ma ya halarci taron.
Your Comment