15 Oktoba 2025 - 08:47
Source: ABNA24
Iran Ta Samu Nasarar Kai Harin Kan Sansanin Isra'ila Na Sirri A Yakin Kwanaki 12

Iran ta harba makami mai linzami a wata cibiyar tsaro ta sirri da ke karkashin wani gini a Tel Aviv a lokacin yakin kwanaki 12, a cewar wani rahoton bincike na wani shafin Amurka.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: Shafin Grey Zone ya wallafa wani rahoto na bincike na wani mai bincike mai suna Jack Paulsen, wanda a baya ya yi aiki a sashen leken asiri na Google kuma ya yi murabus don nuna rashin amincewa da gazawar kamfanin wajen cika alkawuran da ya dauka na kare hakkin dan Adam.

Poulsen ya kuma yi aiki a matsayin mataimakin farfesa a fannin ilmin lissafi da injiniyan lissafi a Jami'ar Stanford da Georgia Tech.

Binciken ya gano cewa shafin ya sami damar gano wani sansanin soja na sirri mai suna "Site 81" da kuma cibiyar hadin gwiwa tsakanin Amurka da Isra'ila da ke karkashin wani ginin hasumiya a wani yanki mai yawan jama'a a arewacin Tel Aviv.

Shafin Grey Zone ya kara da cewa Iran ta kai harin ne a wani hari da makami mai linzami da ta kai kan wasu wurare masu muhimmanci a birnin Tel Aviv a ranar 13 ga watan Yunin 2025. Nan take mahukuntan Isra'ila suka killace wurin tare da hana 'yan jarida ciki har da wakilin Fox News daukar hoton faifan bidiyon wanda aka share shi da karfi da yaji.

A cewar binciken, hasumiya ta DaVinci, wadda makami mai linzami na Iran ya harbo, tana saman cibiyar soji ta sirri, wanda ke kusa da hasumiyar Kinnart na sojojin saman Isra'ila.

Binciken ya nuna cewa Isra’ila ta “kafa sansanonin soji a yankunan fararen hula da ba da makami,” tana kuma sanya takunkumi mai tsauri kan bayananta, sannan tana zargar makiyanta musamman Falasdinawa da “amfani da fararen hula a matsayin garkuwar dan adam, halayyar da ta haramta a karkashin dokokin kasa da kasa.

Binciken ya kuma bayyana cewa, an bayyana shirin fadada wurin mai fadin murabba'in mita 81 zuwa murabba'in 6,000 a cikin takardun gwamnatin Amurka a shekarar 2013, amma har yanzu ba a san takamaiman wurin ba.

Tawagar Grey Zone ta sami damar gano wani hoto da Rundunar Sojojin Amurka na ta dauka a shekarar 2013 da ke nuna aikin gwaji a kan ginin siminti da tsarin karfen wurin. Wannan hoton an dauke shi daga inda Hasumiyar Da Vinci take a halin yanzu.

Your Comment

You are replying to: .
captcha