14 Oktoba 2025 - 15:56
Source: ABNA24
Shaikh Zakzaky Yayi Kiran A Hada Kai Wajen Yakar Kabilanci Da Rugujewar Tattalin Arziki

Shaikh Zakzaky ya kira al'uma da su fuskanci wadannan makirce-makirce na raba kan al’umma, yana mai jaddada cewa hanya madaidaiciya ta shawo kan matsalolin da ake fuskanta ita ce mu koma ga Allah da gaske cikin addu’a da tawakkali, da fatan a karshe zaman lafiya da tsaro za su dawo su tabbata.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: A ranar Lahadi 5 ga Oktoba, 2025, kungiyoyi daban-daban daga jihar Kaduna sun ziyarci gidan Sheikh Ibrahim Zakzaky, jagoran Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), Abuja, domin gaisuwar girmamawa.

Tawagar da ta kai ziyarar, karkashin jagorancin shugabanninsu, sun hada da mutanen Odawa, Birnin Gwari, da Shado, da kuma makwabta. Wanda suka hada da limaman kiristoci na yankin.

A ganawar ta kusan sa'o'i uku da shekh da maziyartan sun tattauna kan matsalolin tsaro da al'ummominsu ke fuskanta sama da shekaru goma, wanda ya raba dubban mutane da muhallansu.

Sun bayyana cewa, sakamakon dan gyare-gyaren da aka samu a fannin tsaro, wasu ‘yan gudun hijirar sun fara komawa garuruwansu.

A nasa martani, Shaikh Zakzaky ya bayyana dalilan da suka sa ta’addancin ke ci gaba da faruwa a Arewacin Najeriya, yana mai alakanta hakan da wata boyayyiyar manufa da nufin amfani da albarkatun kasa masu tarin yawa a yankin.

Ya bayyana damuwarsa kan abin da ya bayyana da gangan na zagon kasa ga ‘yan mulkin mallaka da abokan huldarsu, wadanda suka lalata masana’antun gargajiya kamar su sana’ar kira da saka da sarrafa auduga, a yanzu suna neman wargaza sauran abubuwan more rayuwa kamar noma, kiwo, da kasuwanci.

Shugaban ya kuma bayyana wani shirin sirri na haddasa rikici tsakanin al’ummar Hausawa da Fulani a matsayin hanyar haifar da rikicin kabilanci da kashe-kashen jama’a.

Ya bukaci kowa da kowa – musulmi da wanda ba musulmi ba – da su yi taka tsantsan kada su fada cikin rikicin kabilanci ko addini, ko da a cikin addini daya.

Ya ce, “Lokacin da rikici ya barke tsakanin al’ummomi, wadanda ke amfana kawai su ne wadanda suka yi rura fadan, ba wadanda rikici ya shafa ba.

Shaikh Zakzaky ya kammala jawabinsa da nasiha ga jama’a da su fuskanci wadannan makirce-makirce na raba kan al’umma, yana mai jaddada cewa hanya madaidaiciya ta shawo kan matsalolin da ake fuskanta ita ce mu koma ga Allah da gaske cikin addu’a da tawakkali, da fatan a karshe zaman lafiya da tsaro za su dawo su tabbata.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha