15 Oktoba 2025 - 08:20
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Kai Hari Da Jiragen Yaki Marasa Matuka A Kudancin Lebanon

Kafofin yada labarai sun rawaito cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai wani hari da jiragen yaki marassa matuki a kan wani yanki da ke kudancin kasar Lebanon a ranar Litinin din da ta gabata, lamarin da ke kara bayyana halin da ake ciki na rashin kwanciyar hankali da rashin bin dokar tsagaita wuta da Isra’ila ke yi.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: Kafofin yada labarai na kasar Isra'ila sun bayar da rahoton cewa, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai wani hari da jiragen yaki mara matuki a kan wani yanki da ke kudancin kasar Lebanon a ranar Litinin din da ta gabata, lamarin da ke kara bayyana halin da ake ciki na tsagaita bude wuta da ake yi.

Kafofin yada labaran kasar Lebanon sun ce harin ya faru ne a yankin Hadaya da ke tsakanin Wadi Jello da Yanouh a gundumar Tire da ke kudancin kasar ta Lebanon. Rahotannin farko sun nuna cewa an nufi wani babur ne a harin.

Wannan sabon harin ya zo ne duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka kulla a ranar 27 ga watan Nuwamba, 2024, da kuma kara kai hare-hare na Isra'ila da ke ci gaba da wakana, lamarin da ke kara nuna damuwa kan zaman lafiyar da ake samu da kuma kare lafiyar fararen hula a kudancin Lebanon.

Your Comment

You are replying to: .
captcha