13 Oktoba 2025 - 11:47
Source: ABNA24
Hamas Ta Saki Fursunonin Isra'ila 20

A yau litinin ne aka fara yin musayar fursunoni karo na biyu na musayar fursunoni tsakanin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, inda aka mika fursunonin Isra'ila 13 ga kungiyar agaji ta Red Cross.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya bayar da rahoton cewa: An sako wadannan fursunoni daga tsakiyar Gaza ne. Gidan rediyon Isra'ila ya sanar da cewa, a yanzu babu wani fursuna masu rai a wajen Hamas.

Tun da farko dai da misalin karfe 8 na safe agogon kasar, an gudanar da kashi na farko na musayar fursunoni, inda aka mika fursunonin Isra'ila 7 ga kungiyar agaji ta Red Cross, wanda ya kawo adadin fursunonin Isra'ila da Dakarun Qassam suka mika zuwa yanzu zuwa 20. Hamas ta jaddada cewa, Isra’ila duk da irin karfin da take da shi na leken asiri da karfin soji, ta kasa kubutar da fursunonin ta da karfi.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha