A safiyar yau Lahadi ne filin wasanni na birnin Beirut ya tunbatsa da babban taron kungiyoyin yara’ Rahotanni daga kasar Labanon na cewa, an fara taron ne da aka shafe tsawon watanni ana shirin gudanarwa a safiyar yau Lahadi a dandalin wasanni na birnin Beirut tare da halartar dubun dubatar yara maza da mata daga yankuna daban-daban na kasar Lebanon.
Masu shirya taron sun bayyana cewa, manufarsu ita ce yin mubaya'a ga tafarki da akidar Sayyid Hasan Nasrallah, da kuma nuna hadin kai da zaburar da matasan kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon.
Su ma Kasshafatul Imam Mahdi (A.S) sun zo daga garuruwa daban-daban na kasar Lebanon zuwa filin wasa na Beirut domin halartar wannan taro.
Bikin na yau zai gudana ne karkashin taken "Muna kan alkawarinmu ya Nasrallah" wanda kuma ya kunshi bangarori daban-daban da suka hada da faretin kungiyoyin yara kanana wasannin wake-wake da shirye-shiryen fasaha, da jawabai kan gadon ilimi dana siyasa na shugabannin Hizbullah.
A cewar rahotanni, masu shirya taron suna fatan za a yi wa wannan taro rajista a matsayin "taro mafi girma a duniya".
Kasshafatul Imam Mahdi (A.S) tana daya daga cikin cibiyoyin al'adu da ilimi da ke da alaka da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, wadda ta fara gudanar da ayyukanta tun a shekarun 1980, kuma a yau tana ci gaba da yaduwa a yankuna daban-daban na kasar Lebanon, musamman a tsakanin iyalai da ke goyon bayan Hizbullah.
Baya ga shirye-shiryen al'adu da ilimi, wannan al'umma kuma tana taka rawar gani wajen shirya bukukuwan addini da na kasa.
Your Comment