14 Oktoba 2025 - 13:23
Source: ABNA24
Hamas: Falasdinawa 5 Sun Yi Shahada A Gaza | Isra’ila Ta Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta

Majiyar Falasdinu ta rawaito cewa jiragen yakin Isra'ila na ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Jiragen yakin na maharan sun kai hari a unguwar "Shuja'iya" da ke gabashin birnin Gaza inda suka kashe 'yan Falasdinawa biyar.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: Kakakin kungiyar Hamas Hamaz Qassem ya sanar da cewa sojojin yahudawan sahyoniya sun karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta hanyar shahadantar da wasu 'yan kasar a Zirin Gaza ta hanyar jefa bama-bamai da harbe-harbe a safiyar yau.

Ya kara d acewa: "Haka kuma, muna kira ga dukkan bangarorin da ke shiga tsakani da su sanya ido kan halayyar 'yan mamaya, kada su bari Isra'ila ta karya alkawuran da ta dauka ga masu shiga tsakani dangane da kawo karshen yakin zirin Gaza".

Majiyoyin labaran Falasdinu sun ba da rahoton ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da jiragen yakin Isra'ila suka yi. A ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila kai hari tare da shahadantar da wasu 'yan kasar Falasdinu a unguwar "Shuja'iya" da ke gabashin birnin Gaza, lamarin da ya yi sanadin shahadar mutane 5.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha