14 Oktoba 2025 - 10:02
Source: ABNA24
PM Pakistan: Tsagaita Wuta A Gaza Ya Ceci Miliyoyin Rayuka

A makon da ya gabata ne Trump ya sanar da cewa, Isra’ila da Hamas sun amince da kashi na farko na shirin da ya tsara a ranar 29 ga watan Satumba na samar da tsagaita bude wuta a Gaza, da sakin daukacin fursonin Isra’ila da Hamas ke tsare da su, domin musayarsu da fursunonin Falasdinu, da kuma janyewar sojojin Isra’ila a hankali daga daukacin yankin Zirin Gaza. Kashi na farko na yarjejeniyar ya fara aiki ranar Juma'a.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa:  Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif a ranar Litinin ya ce cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza ya ceci miliyoyin rayuka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Da yake jawabi a wajen taron zaman lafiya na Gaza a birnin Sharm el-Sheikh na kasar Masar, karkashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi, Sharif ya yaba da rawar da Trump, da shugaban kasar Turkiyya Erdogan, da yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohamed bin Salman da sauran shugabannin kasashen duniyaa da suka taka wajen bayar da gudunmowa ga yunkurin samar da zaman lafiya.

Ya sake nuna ra’ayinsa na cewa Trump ne ya kamata a bawa lambar yabo ta Nobel don samar da "zaman lafiya" a kudancin Asiya, saboda cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

A cewarsa Pakistan ta zabi Trump a matsayin wanda ya kamata a bawa lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel saboda "fitaccen gudummuwar da ya bayar wajen dakatar da yakin da ke tsakanin Indiya da Pakistan da farko, sannan a cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da babbar tawagarsa".

Sharif ya kara da cewa, "A yau kuma, ina son na sake nuna ra’ayina ga zabar babban shugaban kasar Amurka na ba shi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, domin a hakika ina jin cewa shi ne ya fi kowa nagarta kuma mafi dacewa don samun kyautar zaman lafiya, domin ba wai kawai ya samar da zaman lafiya a kudancin Asiya ba, ya ceci miliyoyin mutane, da rayukansu, kuma a yau, a Sharm el-Sheikh, ya samar da zaman lafiya a Gaza tare da ceto miliyoyin rayuka a yankin Gabas ta Tsakiya".

A makon da ya gabata ne Trump ya sanar da cewa, Isra’ila da Hamas sun amince da kashi na farko na shirin da ya tsara a ranar 29 ga watan Satumba na samar da tsagaita bude wuta a Gaza, da sakin daukacin fursonin Isra’ila da Hamas ke tsare da su, domin musayarsu da fursunonin Falasdinu, da kuma janyewar sojojin Isra’ila a hankali daga daukacin yankin Zirin Gaza. Kashi na farko na yarjejeniyar ya fara aiki ranar Juma'a.

Matakin na biyu na shirin ya kunshi kafa sabuwar tsarin mulki a Gaza, da kafa runduna ta kasa da kasa, da kuma kwance damarar Hamas.

Da sanyin safiyar litinin ne aka fara sakin Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen yari na Isra'ila bayan da kungiyar Hamas ta saki dukkan fursunonin Isra'ila guda 20 da ake tsare da su a zirin Gaza.

Your Comment

You are replying to: .
captcha