10 Oktoba 2025 - 14:47
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Ƙi Amincewa Da Sakin Wasu Manyan Kwamandojin Falasdinawa Shida

Jaridar Yedioth Aharonot ta bayar da rahoton cewa, mahukuntan Isra'ila sun ki yarda da sakin wasu manyan kwamandojin Falasdinawa shida a wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni - wanda ke cikin shirin tsagaita bude wuta da Donald Trump ya yi na kawo karshen yakin Gaza.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cewar rahoton, Tel Aviv na daukar wadannan mutane a matsayin "jajen layi" a kowace yarjejeniyar musayar fursunoni. Yayin da sakin hudu daga cikinsu na daya daga cikin manyan bukatun kungiyar Hamas, gwamnatin Isra'ila ta hana a sake su ta hanyar yin watsi da batunsu.

Sunayen kwamandojin guda shida kamar haka: Marwan al-Barghouthi, Ahmed Saadat, Abbas al-Sayed, Ibrahim Hamed, Abdullah al-Barghouthi da Hassan Salameh.

Your Comment

You are replying to: .
captcha