Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt {As} –ABNA- ya habarta cewa: kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Palasdinawa ta Hamas da masu shiga tsakani sun sanar da cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma gwagwarmayar Palasdinawa sun cimma matsaya kan mataki kashi na farko na shirin Amurka na kawo karshen yakin Gaza.
Shugaban Amurka Donald Trump ya rubuta a cikin wani sako ta kafar sada zumunta ta Truth Social cewa: Yau rana ce mai girma ga kasashen Larabawa da Musulunci, Isra'ila da Amurka, muna godiya da rawar da masu shiga tsakani na kasashen Qatar, Masar da Turkiyya suka taka. Ya kuma jaddada cewa an cimma wannan yarjejeniya ta hanyar da ta dace ga dukkan bangarorin.
Trump ya kara da cewa: A bisa wannan yarjejeniya, nan ba da jimawa ba za a cimma nasarar sakin dukkan fursunonin, sannan sojojin Isra'ila za su janye zuwa layukan iyaykokin da aka amince da su; wannan shi ne matakin farko na samun dauwamammen zaman lafiya mai karfi.
Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta kuma sanar da cewa, a tattaunawar da aka yi a birnin Sharm el-Sheikh, an cimma matsaya kan aiwatar da kashi na farko na tsagaita bude wuta; yarjejeniyar da za ta kai ga dakatar da yakin da kuma sako fursunonin Falasdinu da Isra'ila.
Kafofin yada labaran yahudanci, ciki har da tashar Channel 12, sun ba da rahoton cewa, za a rattaba hannu a kan yarjejeniyar a hukumance a yau (Alhamis), kuma mai yiwuwa kashi na farko na sakin fursunonin zai fara ne a ranar Asabar ko Lahadi.
Matsayar Hamas: Cikakkiyar Janyewa Da Musayar Fursunoni
Har ila yau kungiyar Hamas ta sanar a cikin wata sanarwa cewa, an cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin da ake yi a Gaza, da kammala janye sojojin mamaya, da shigar da kayan agaji, da musayar fursunoni. Hamas ta jaddada cewa yarjejeniyar ta samo asali ne sakamakon tattaunawa mai daukar hankali da gaske a cikin tsarin shirin Trump da aka gabatar a Sharm el-Sheikh.
Sanarwar ta ce: "Mun yaba da kokarin 'yan'uwa masu shiga tsakani a kasashen Qatar, Masar, da Turkiyya, da kuma kokarin shugaban Amurka Donald Trump na kawo karshen yakin baki daya da kuma janye gwamnatin mamaya daga zirin Gaza".
Hamas ta kuma yi kira ga gwamnatin Amurka, da kasashen da suka amince da yarjejeniyar, da sauran bangarorin Larabawa, na Musulunci, da na kasa da kasa, da su tilasta wa gwamnatin sahyoniyawan aiwatar da alkawurran da ta dauka, ba tare da barin gwamnatin ta ki amincewa ko jinkirta yarjejeniyar ba.
A karshen bayanin nata, kungiyar Hamas ta yi jawabi ga al'ummar Palastinu tare da bayyana cewa: Al'ummarmu mai girma a Gaza, Qudus, Yammacin Kogin Jordan, a cikin kasar Palastinu mai dimbin tarihi, da ma duniya baki daya, gwagwarmaya tsayin daka da sadaukarwa mara misaltuwa, ta dakile shirin 'yan mamaya da rashin mika wuya da kuma tilasta kauracewa gidajenku. Za mu tsaya tsayin daka kan wannan alkawari kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai an sami cikakken 'yanci da tabbatar da 'yancin kai.
Majiyar Masar ta sanar da cewa, bisa yarjejeniyar da aka cimma, manyan motocin dakon kayan agaji 400 za su shiga yankin zirin Gaza a kullum cikin kwanaki biyar na farko bayan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta.
Martanin Isra'ila/ Isra'ila Ta Bawa Sojojinta Umarnin Janyewa Zuwa Layukan Da Aka Sanar A Yarjejeniyar Gaza.
A gefe guda kuma Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa majalisar ministocin kasar za ta yi zama a yau domin amincewa da yarjejeniyar a hukumance tare da dawo da fursunonin Isra'ila. Ya ce: Za mu cimma manufofinmu da karfi da karfafa zaman lafiya da makwabtanmu.
Kakakin sojin Isra'ila ya sanar da bayar da umarnin janyewar sojojin Isra'ila zuwa layukan da aka sanar a yarjejeniyar Gaza.
Kakakin rundunar sojin Isra'ila ya kuma sanar da cewa, bisa umarnin shugabannin siyasa da kuma kimanta halin da ake ciki, sojojin sun fara shirye-shiryen aiwatar da yarjejeniyar, kuma a lokaci guda suna gudanar da shirye-shirye da matakan yaki don matsawa zuwa iyakar sojojin da aka yi wa kwaskwarima nan gaba kadan.
Your Comment