A 'yan watannin baya-bayan nan dai dakarun sojin Yamen sun kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke da alaka da gwamnatin sahyoniyawan da kawayenta a tekun Bahar Maliya, ta hanyar amfani da jiragen yaki marasa matuka da makamai masu linzami. Wadannan hare-hare dai wani bangare ne na dabarun karya tattalin arziki da soja ga Isra’ila domin matsin lamba ga mahukuntan mamaya da kuma tallafawa al'ummar Gaza.
Manyan kamfanonin sufurin jiragen ruwa sun sanar da cewa, komawa ga gajeriyar hanya mai muhimmanci ta kogin Suez zai yiwu ne kawai bayan an kafa tsagaita bude wuta na dindindin tare da tabbatar da cikakken tsaro a yankin, in ba haka ba, wadannan kamfanoni za su zabi hanyar da ta fi tsayi ta hanyar Cape of Good Hope a kudancin Afirka a matsayin madadin.
Barazanar Tsaron Sojojin Yemen A Kan Jiragen Ruwa
Sojojin Yamen suna kai hare-hare kan jiragen ruwa na soji da na kasuwanci masu alaka da Isra'ila da kawayenta wanda su ke amfani da jirage marasa matuka da makamai masu linzami wajen wannan hare-hare, wanda wani bangare ne na dabarun Yaman na tinkarar mamayar Gaza da kuma goyon bayan gwagwarmayar Palastinawa, kuma masana harkokin tsaro na ganin cewa matsin lambar teku da na tattalin arziki na iya tilasta wa gwamnatin sahyoniyawan dakatar da kai hare-hare a Gaza.
Dakatar da jiragen ruwa masu ratsa tekun Bahar Rum, na daya daga cikin muhimman hanyoyin safarar ruwa a duniya, ya yi tasiri sosai a harkokin cinikayyar duniya, kuma amfani da wasu hanyoyin ya kara tsadar sufuri da kuma bata lokaci, lamarin da ya kawo cikas ga tsarin samar da kayayyaki a yankunan da aka mamaye.
Matsayin Yanayin Kasar Yemen Ga Gaban Yanki
Kasar Yemen dai na taka muhimmiyar rawa a harkokin tsaro da ci gaban tattalin arzikin yankin, saboda yanayin da take da shi na mallakar mashigar Babul-Mandab da kuma tekun Red Sea. Sarrafa wannan muhimmin mashigar yana da matukar mahimmanci ga duk masu iko da yanki da na duniya.
Martanin Ƙasashen Duniya Da Hasashen Gaba
Duk da matsin lamba da kasashen yammacin duniya musamman Amurka suke yi na tabbatar da tsaron jiragen ruwa masu alaka da gwamnatin sahyoniyawan, kawo yanzu hare-haren da sojojin Yamen ke kaiwa ba su tsaya ba, kuma kamfanonin sufurin jiragen ruwa na yin taka-tsantsan tare da zabar wasu hanyoyi.
Wadannan kamfanoni sun sanar da cewa, har sai an tabbatar da tsagaita bude wuta na dindindin da kuma tabbatar da tsaron hanyar tekun Bahar Maliya kana kamfanonin sufurin jiragen ruwa za su wucewa ta wannan muhimmiyar hanya, wadda ta shafi kasuwancin duniya.
Your Comment