8 Oktoba 2025 - 08:51
Source: ABNA24
Isra’ila Ta Kai Hari Kan Jirgin Ruwan Agaji Na Gaza

Kwamitin kasa da kasa don kawo karshen killace Gaza ya sanar da cewa "Sojojin Isra'ila sun kai hari kan Freedom Flotilla a cikin ruwan kasa da kasa mai nisan mil 120 daga Gaza".

A sa’I daya kuma tawagar "jiragen Somod" ta sanar da cewa ana gallazawa da dama daga cikin masu fafutukar a gidajen yarin Isra’ila, ciki har da mai fafutukar kare muhalli Greta Thunberg ta Sweden, wacce ta shiga cikin tawagar ta Somod Flotilla.

A cewar tawagar, daya daga cikin wadanda ake tsare da su ya ce: "An hana ni tsaftataccen ruwan sha, sannan sauran wadanda ake tsare da su ma an hana su magunguna masu muhimmanci".

Kungiyar gwagwarmayar ta Flotilla ta kara da cewa a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce har yanzu mambobi shida na cikin jirgin na hannun sojojin Isra'ila; Mutanen da a cewar kungiyar, an yi garkuwa da su ba bisa ka'ida ba a cikin ruwan kasa da kasa.

Your Comment

You are replying to: .
captcha