10 Oktoba 2025 - 21:34
Source: ABNA24
Amurka Ta Janye Muhimman Takunkumai Kan Kasar Siriya

Majalisar Dattawan Amurka Ta Dage Takunkumin Kaisar Kan Syria

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt {As} –ABNA- ya habarta cewa: Majalisar dattijan Amurka ta zartar da wani kudiri na dage wani bangare na takunkumin da ake kira "Kaisar" kan Syria. Wadannan takunkuman da aka fara aiwatar da su tun lokacin mulkin Bashar al-Assad, sun hada da tsauraran takunkumi kan cibiyoyin gwamnatin Syria, bankuna, kamfanonin mai da makamashi, da kuma sassan kadarori da fitar da kayayyaki.

An aiwatar da dokar kakaba takunkumin Kaisar ne a wa'adin farko na Donald Trump don hukunta Damascus saboda abin da ta kira "gaggarumin take hakkin dan Adam a lokacin yakin basasar Siriya," kuma tsawon shekaru yana hana hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin sauran kasashe da Siriya.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha