Dangane gudanar da taron Sallah karo na 32 da sako na da Imaminmu mai daraja, ina son kawo wasu 'yan bayanai game da muhimmancin Sallah a wannan taro: Sallah ta fi dukkan ibadu ta tattaro dukkan cikakkun kalmomi ita ce mabubbugar dukkan ni'ima da albarka, kuma da barinta ne mabudan dukkan matsaloli suke budewa. Saboda muhimmancinta kimanin ayoyi 122 ne aka kebe ta da su a cikin Alkur’ani mai girma. Itace tushen Ibadu kuma mai muhimmanci da aka nanata tare da tabbatar da a cikin dukan addinan sama. Daya daga cikin ayoyin da aka ambata game da sallah ita ce aya ta 103 a cikin suratun Nisa'i:
فَإِذَا اطْمَأْنَنْتُمْ فَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ إِنَّ الصَّلَاةَ كَانَتْ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ كِتَابًا مَوْقُوتًا (103)
Allah Ta’ala Ya ce: “Kuma Ku Tsaida Sallah Domin Ita Sallah Farilla Ce Tabbatacciya Akan Muminai Wacce Take Da Takamaiman Lokaci”. Ya zo a cikin ruwaya daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Farkon abin da Allah Ya wajabta wa bayinsa ita ce salla, kuma karshen abin da ya wajabtawa bawa har zuwa lokacin mutuwa ita ce salla, abin da za a fara tambayar bawa da yi masa hisabi a ranar kiyama ita ce salla, idan mutum ya yi ta daidai, to zai shiga Aljanna, idan kuma ba a yi ta ba daidai, to lallai za’a jefa shi wuta ne. Domin alamar bauta da kasancewa bawan Allah shi ne yin sallah, dukkan sauran ibadu ana iya daga kafa ga barin yinsu su alokacinsu amma ban da sallah domin ba za a iya dakatar da yin ta ba a cikin kowane hali, ko da kuwa mutum yana yanin da kawai zai iya motsa idanunsa ne to ta wajaba a kansa, a cikin suratu Taha aya ta 14, yana cewa:
إِنَّنِي أَنَا اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدْنِي وَأَقِمِ الصَّلَاةَ لِذِكْرِي (14)
"Lallai Ni Ne Allah, Babu Abin Bautawa Face Ni, Ku Bauta Mani Kuma Ku Tsaida Sallah Domin Anbatona” ma’ana ku kasance bayina wanda alamar hakan shine tsaida sallah domin anbatona, to kenan dukkan wanda baya yin sallah bai ainta da yarda da kasancewa bawana ba. Saboda hakane ma dukkan ayyukan da yayi na kirki ba za’a bincikaa ba indai sallarsa bata karbu ba kuma za’’a tura shi ne Jahannama. Manzon Allah (S.A.W) ya fada a cikin ruwayoyi masu yawa cewa duk wanda ya bar sallah da gangan to kafiri ne kuma ba shi da wani rabo a cikin musulunci, daya daga cikin muhimman tasirin da sallah ke da shi, shi ne samun aminci da nutsuwa, wanda ya zo a cikin suratu Ra'ad, aya ta 28, yana cewa:
الَّذِينَ آمَنُوا وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُمْ بِذِكْرِ اللَّهِ أَلَا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ (28)
"Wadanda suka yi imani kuma zukatansu suke samun nutsuwa da anbaton Allah domin da anbaton Allah ne zukata suke samun nutsuwa". Kun kenan anan kamar yadda cewaa surar Daha: “Ku tsai da salla, domin ambatona. Ayoyi biyu sun fassara anbaton Allah da yin sallah. Ba za ka taba samun wanda ba ya sallah a doron kasa yana zaune lafiya cikin aminci da nutsuwa da akwanciyar rai ba”. Tabbas ba dukkan masu ibada ba ne suke zaman lafiya domin sallar wasu daga cikinsu ba ta gaskiya ba ce kuma ba ta isa ta ba su cikakkiyar lafiya ba, ko shakka babu ba wai dukkan masu yin sallah ba ne ssuke samun nutsuwa da aminci ba domin sallar wadansu daga cikinsu ba ta hakika ba ce da zata iya basu nutsuwa da aminci gaba daya cikakke. Duk da cewa Sallah tana tasiri da yawa a duniyarmu, ciki har da rigakafin cututtuka daban-daban da tasiri ga arziki da samun dawata aa rayuwa da albarkar rayuwa, wadanda aka tabbatar da su a kimiyance da addinance, kuma wadanda suke so za su iya yin bincike kan wadannan al’amura.
Ga takaitaccen sakon Masoyinmu Imam jagoran juyin juya halin musulunci na Iran danagen da taron Sallah yana kunshe da abubuwa masu matukar muhimmanci, inda yake cewa: Makomar mutum a duniya da lahira ya dogara ne da yin sallah , wacce yin ta da kaskantar da kai da bzayar zuciya ga Allah, yana kawo aminci, da karfafar irada, da rayar da fata. Ya ce ya kamata yayi iyaye, malaman addini da malamai da duk hukumomin yada addini da dukkan masu addini su dauki nauyin gudanar da sallar da koyar da ita ta hanyar amfani da sabbin kayan aiki da karfafa gwiwa.
Tsakure daga Hudubar Sallar Juma'a ta wannan makon (10/10/2025) a birnin Alishah da Hujjutul-Islam Hamidinejad, limamin birnin Sallar Juma'a na wannan birni.
Your Comment