Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Shugaban kungiyar ceton yara ya ce wannan mummunar girgizar kasa da ta afku a yankunan gabashin kasar Afganistan, musamman lardin Kunar, baya ga hasarar rayukan da aka yi wa dubban mutane, ya kuma haifar da bukatar agajin gaggawa.
A cewar sanarwar da kungiyar ta buga a ranar Alhamis, 11 ga watan Satumba, sama da yara 200,000 a yankunan da girgizar kasar ta shafa na bukatar agajin gaggawa.
Sanarwar ta ce sama da yara mata 500 da yara maza 650 na daga cikin wadanda suka mutu.
Gidajen mutane sama da 38,000, wadanda kusan rabinsu yara ne gaba daya sun lalace.
"Yaranmu ba su da tufafi, komai yana karkashin tarkace, ba su da komai," haka wani mahaifin wadanda abin ya shafa ya shaida wa kungiyar.
Samira Sayed Rahman, Babban Manajan Tallafi na ceton yara Afganistan ya ce "Abubuwan da aka fi bukata ga yara a yankunan da girgizar kasar ta shafa sun hada da abinci, matsuguni da ruwa mai tsafta." "Amma bayan lokaci, iyalai da suka rasa gidajensu da rayuwarsu za su buƙaci dawwamammen tallafi don sake gina rayuwarsu".
Kungiyar ceton Yaran ta yi kira ga kasashen duniya da kungiyoyin agaji da su ba da agaji cikin gaggawa, wadanda suka hada da abinci, matsuguni na wucin gadi da kuma samar da cibiyoyin kiwon lafiya.
Kungiyar ta kuma jaddada cewa yara musamman a lunguna da sako na cikin hadarin kamuwa da cututtuka da rashin abinci mai gina jiki kuma suna bukatar kulawa ta musamman.
Girgizar kasar wadda ta kasance daya daga cikin bala'o'i mafi muni da aka taba fuskanta a kasar ta Afganistan a cikin 'yan shekarun nan, ta sake bayyana nakasuwar ababen more rayuwa da karancin hanyoyin shiga yankunan karkara a kasar.



Your Comment