9 Satumba 2025 - 22:18
Source: ABNA24
Iran: Ta Cimma Matsaya Tare Da Hukumar Nukiliya Ta Duniya

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya sanar da kammala fahimtar juna tsakanin Iran da hukumar a wata hira da ya yi da kafar yada labaran cikin gida.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya sun cimma fahimtar juna kan yadda za su ci gaba da yin mu'amala a cikin sabon yanayin, biyo bayan hare-haren haramtacciyar kasar Isra'ila da Amurka kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran.

A yammacin yau ne aka gudanar da tattaunawa tare da ministan harkokin wajen kasar Iran da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya a birnin Alkahira. Za a sanar da cikakkun bayanai game da wannan tattaunawa da matsayar da suka cimmawa nan da ɗan lokaci kaɗan a taron manema labarai na Ministan Harkokin Wajen ƙasar Iran.

Dan gane da sanya hannu kan yarjejeniyar dawo da hadin gwiwa tsakanin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da Iran shima 

Raphael Grossi babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ya tabbatar da cewa: Mun cimma yarjejeniya da ministan harkokin wajen kasar Iran kan daukar matakai masu amfani don ci gaba da gudanar da bincike a kasar Iran, kuma ana daukar wannan mataki mai muhimmanci a kan hanyar da ta dace.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha