Babban shugaban kungiyar Hizbullah ya yi magana ga kasashen Larabawa da cewa: Ku da baku da ikon maida martanin soji ga Isra'ila Alal akallah ku goyon bayan gwagwarmaya mana.
Idan gwagwarmaya ta durkushe, Isra'ila wajenku zata yo. don haka goyon bayan gwagwarmaya na nufin goyon bayan gwamnatin ku da kasar ku. Kada ku soki gwagwarmaya a baya ta hanyar tsayawarku tare da Isra'ila kuma kada ku yi kokarin kwance damarar gwagwarmayar Palasdinawa da kuma yarda da sharuddan sahyoniyawa.
Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ya cikin shirinta na aiwatar da shirin “Babbar Isra’ila”, watakila wata rana za mu ji an kai wa Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa hari. Amurka na son kwance damarar gwagwarmaya da kuma mayar da kasar Lebanon ta zama miya mai man shanu ga Isra'ila; idan har hakan ta faru, yahudawan sahyoniyawa za su zo Lebanon don aiwatar da shirin Babbar Isra'ila.
Your Comment