Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Rundunar Qassam reshen soji na Hamas, ta fitar da wasu hotuna a yau Alhamis na harin da ta kai kan wata tankar yaki ta Merkava tare da dasa bam a cikin wurin matukin tankar da ke tsakiyar Jabalia, a arewacin zirin Gaza. A wannan farmakin, sojojin mamaya sun tabbatar da kashe sojoji hudu.
Dakarun Qassam sun rubuta yadda aka shirya da dasa bam din kafin aikin, inda suka ga wata tanka a yankin Al-Omari da ke tsakiyar Jabalia, sannan wani mayaki ya shiga cikin tankin ya jefa bam din a cikin dakin matukin wanda ke matsayi na jarumtakarsu.
Bidiyon ya kuma nuna fashewar tankar da hayakin fashewar, wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Isra'ila hudu a cikin tankar da ke konewa.
Asa + Musa
A karshen faifan bidiyon, rundunar Qassam ta tabbatar da cewa "kamar yadda aka saba, za mu sake maimaita yin hakan".
A ranar litinin da ta gabata majiyoyin yahudawan sun tabbatar da mutuwar sojojin Isra'ila hudu a wani harin bam da dakarun Palasdinawa suka yi a zirin Gaza. Lamarin dai ya zo daidai da wani harin shahada da aka kai a birnin Kudus wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji shida da yan share guri zauna.
Majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na safe kusa da Jabalia, lokacin da aka jefa bam a kan ma’aikatan wata tankar. Tankar ta kama wuta, inda ta kone dukkan ma'aikatanta.
Your Comment