10 Satumba 2025 - 23:19
Source: ABNA24
Hoton Khalil al-Hayya Sa'o'i Bayan Harin da Isra’ila Ta Kai A Qatar

Majiyoyin yada labarai sun wallafa hoton daya daga cikin manyan shugabannin kungiyar Hamas, sa'o'i kadan bayan harin ta'addancin da gwamnatin sahyoniya ta kai wa Qatar.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) nakalto daga shafin sadarwa na Sudal Balad cewa, sa'o'i kadan bayan harin da gwamnatin sahyoniyawa ta kai birnin Doha, an buga hoton wannnan babban shugaban a kungiyar Hamas a gadon asibiti, wanda ya ke nuni da yatsunsa alamar nasara ko shahada. Amma bayar da wani karin bayani kan lamarin.

Idan dai ba a manta ba, kafin wannan lokacin, kungiyar Hamas ta sanar da gazawar gwamnatin sahyoniyawan na harin ta'addancin da ta kai na kashe shugabannin Hamas a birnin Doha na kasar Qatar.

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Palasdinawa ta Hamas ta fitar da sanarwa tana mai cewa: Mummunan yunkurin da gwamnatin sahyoniyawan sahyoniya ta yi na kashe tawagar shiga tsakani na Hamas a babban birnin kasar Qatar babban laifi ne, da kuma keta dokokin kasa da kasa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, mun dauki wannan laifin a matsayin wani hari kan diyaucin kasar Qatar, kasar da tare da Masar, ke taka muhimmiyar rawa wajen inganta shiga tsakani da kokarin kawo karshen mamayar da kuma cimma yarjejeniya kan tsagaita bude wuta da musayar fursunoni. Wannan matakin ya sake fallasa irin laifuffukan yana mamaya da kuma aniyarsu ta lalata duk wata yarjejeniya.

Hamas ta ci gaba da cewa: "Muna bayyanawa karara cewa makiya sun gaza a yunkurinsu na kashe 'yan uwanmu a fagen aikinsu na samara da sulhu, yayin da wasu 'yan uwanmu shahidai suka shiga sahun daukaka da daraja ta shahada:

Shahida Jihad Labad

Shahidi Humam al-Hayya

Shahidi Abdullah Abdel Wahed

Shahid Momen Hassouna

Shahidi Ahmed al-Mamlouk

Muna kuma mika ta'aziyyarmu ga shahadar "Badr Saad Muhammed al-Humeidi" daya daga jami'an tsaron cikin gida na Qatar.

Your Comment

You are replying to: .
captcha