Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ma'aikatar shari'a ta sanar da cewa: An gabatar da wata tuhuma kan jami'an leken asirin gwamnatin Isra'ila 4 da ke da alaka da Mossad.
Wadanda ake tuhumar su 4 sun aikata ayyukan laifuka kamar daukar hotuna da bidiyo da aika su ga jami’an Mossad don gano daidai wuraren sojoji da kagarorin jami'an tsaron Iran, da cibiyoyi masu muhimmanci, tare da samar da katin SIM da siyan wayoyi na musamman don kiran taron gaggawa da wakilan makiya, da haddasa fashewar abubuwa da tayar da gobara musamman a biranen Tehran da Arumiyyeh da Shahrod, da Isfahan da ma dukkan fadin kasar, a maimakon wannan hidima sun karɓi makudan kuɗi daga sojojin Isra'ila a cikin nau'ikan tsarin tura kuɗi na cryptocurrency.
Your Comment