Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ministan harkokin wajen Qatar Mohammed bin Abdulrahman ya ce: A halin yanzu muna tattaunawa da takwarorinmu na yankin kan matakin mayar da martani kan harin na Isra'ila.
A ci gaba da tattaunawa da kafar yada labaran kasar Amurka CNN, ya ce Doha na sake yin nazari kan komai game da rawar da ta taka da kuma makomar kungiyar Hamas a Qatar.
Shi ma Firaministan Qatar ya ce yayin da yake ishara da abinda ya faru: a yau, dukkanin yankin tekun Farisa na cikin hadari. Kuma tabbas za mu mayar da martani kan harin da Isra'ila ta kai a Doha
Ya kara da cewa: Domin Netanyahu yana barazana ga kasashen yankin yayin da basu yi masa wata barazana ba.
An ci amanar mu, Abin da Isra'ila ta yi shi ne ta'addanci na kasa kuma ba zan iya bayyana girman fushina ba. Domin Netanyahu yana lalata duk wata dama ta samun kwanciyar hankali da zaman lafiya kuma yakamata a gurfanar da shi a matsayin wanda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema ruwa a jallo. Kawai Netanyahu yana bata lokacin mu ne akan yin sulhu kuma ba da gaske ya ke ba. In ji shi.
Kasar Qatar dai na fatan za a mayar da martani da baki daya kan harin da Isra'ila ke kaiwa jami'an Hamas a Doha.
Bisa wannan lamari ana sa ran za a gudanar da taron kasashen Larabawa da Musulunci a Doha a kwanaki masu zuwa domin amincewa da matakin da za a dauka. Domin dole za a samu martani daga yankin kuma a halin yanzu ana tuntubar juna da tattaunawa da sauran abokan hulda.
Your Comment